Gwamnatin Tarayya Ta Sauya Tunani Kan Shirin Cire Tallafin Man Fetur
- Gwamnatin tarayyan Najeriya ta dakatar da shirin cire tallafin man fetur a karshen mulkin shugaba Muhammadu Buhari
- Majalisar tattalin arziki ta ƙasa (NEC) a taron da ta gudanar yau ta ce bai kamata a cire tallafin ba a halin yanzu
- Ministar kuɗi, Zainab Ahmed, ta ce NEC ta aminta cewa za'a ci gaba da tattauna wa kan batun da wakilan jihohi
Abuja - Majalisar tattalin arziki ta gwamnatin Najeriya (NEC) ta dakatar da shirin zare tallafin Man Fetur a karshen gwamnatin shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari.
Ministar kuɗi, kasafi da tsare-tsaren ƙasa, Zainab Ahmed, ce ta bayyana haka yayin zantawa da 'yan jaridan gidan gwamnati jim kaɗan bayan kammala taron NEC.
Rahoton Vanguard ya ce taron NWC ɗin ya gudana karkashin jagorancin mataimakin shugaban ƙasa, Farfesa Yemi Osinbajo, a Aso Villa, birnin tarayya Abuja.
Zainab Ahmed ta ƙara da bayanin cewa shirin cire tallafin Man Fetur ɗin zai fara aiki ne daga watan Yuni, 2023 saboda kasafin kuɗin 2023 ya ware tallafin har zuwa watan Yuni.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
A cewarsa duk wani jinkiri na cire tallafin da aka samu zai bukaci garambawul a kundin dokokin man Fetur (PIA) da kuma kasafin kuɗin wannan shekarar da muke ciki.
Ministan ta ce babu wani sabon wa'adin cire tallafin da NEC ta sanya, a halin yanzun sun bar wuƙa da nama hannun gwamnati mai zuwa, ita zata yanke cirewa ko akasin haka.
Matsayar da NEC ta cimma a taronta
Misis Ahmed ta ce taron NEC ya karkare cewa yanzun ba lokacim da ya dace bane a cire tallafin Man Fetur, "Don haka kowa ya aminta cewa ba za'a cire ba a yanzu."
Amma majalisar tattalin arziƙin ta amince cewa za'a ci gaba da tattauna wa kan batun da haɗin guiwar wakilan jihohi da kuma sabuwar gwamnatin da zata hau kan mulki nan gaba.
Channels tv ta tattaro cewa batun cire tallafin man fetur a Najeriya yana da ruɗani, wasu na ganin bai da amfani yayin ɗa wasu kuma ke ganin talaka abun zai wa illa.
Femi Adesina Ya Bayyana Dalilin Kasa Cika Wasu Alkawura Da Buhari Ya Yi
A wani labarin kuma Gaskiya Ta Bayyana Kan Dalilin Da Ya Sanya Shugaba Buhari Ya kasa Cika Wasu Alkawuran Da Ya Yi Wa 'Yan Najeriya
Fadar shugaban ƙasa ta ce shugaba Muhammadu Buhari bai san da wasu alƙawurra da kungiyoyin magoya bayansa suka ɗaukarwa yan Najeriya ba.
Asali: Legit.ng