Jirgin saman NigeriaAir Zai Fara Tashi Kafin Shugaba Buhari Ya Bar Aso Rock – Minista
- Daga yanzu zuwa 29 ga watan Mayu, za a iya ganin jirgin saman NigeriaAir yana yawo a samaniya
- Hadi Sirika ya tabbatarwa ‘Yan Najeriya gwamnati ba ta hakura da maganar samar da jirgin sama ba
- Ministan harkokin jiragen ya ce samun kamfanin jirgi na gida zai bunkasa tattalin arzikin Najeriya
Abuja - Ministan harkokin jiragen sama, Hadi Sirika yana nan a kan bakarsa na cewa jirgin saman NigeriaAir zai fara tashi kafin karshen Mayun bana.
A ranar Laraba Daily Trust ta rahoto Hadi Sirika ya ce an kammala duk wasu shirye-shirye da ake bukata domin jirgin saman na Najeriya ya fara aiki.
Da ‘yan jarida suka yi magana da shi bayan taron FEC da aka yi a fadar Aso Rock, Ministan ya ce jirgin zai tashi kafin Muhammadu Buhari ya bar ofis.
Manema labarai sun tuntubi Ministan harkokin jiragen sama domin jin inda aka kwana, ganin saura kusan wata guda gwamnati mai-ci ta shude.
Magana ta na nan har gobe
Sanata ya nuna babu dalilin da zai janye kalamansa, gwamnati za ta cika alkawarin na ta.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
The Nation rahoto Ministan ya ce a Fubrairu shugaban kasa ya hadu da shugabannin kamfanonin Girma Wake da Ethiopian Airlines a kan shirye-shiryen.
Jawabin Hadi Sirika
“Na fada cewa kamfanin Nigeria Air Limited zai fara aiki kafin karshen wa’adin gwamnatin nan, kuma ban janye kalamai na ba.
Mun tanadi duk abubuwan da ake bukata, jiragen na nan, akwai ofisoshi da cibiyoyin aiki da ma’aikata da duk abin da ake bukata.
Mu na karasa abubuwan da suka rage ne sannan mu jira takardar AOC, sai jirgi ya fara tashi.
Zai tashi, kuma saboda cigaban kasar nan ne, la’akari da yawan al’umma da adadin masu tafiya-tafiye, da yadda zai bunkasa tattali.
Musamman ta bangaren yawan bude idanu, hada-kan Afrika da manufar kungiyar AU ta 2063.
Wannan muhimmin aiki ne kuma dole in fada, hakan zai tabbata kafin karshen mulkinmu nan da makonni hudu da kwanaki biyu.
- Hadi Sirika
Za a tattaro wadanda ke Sudan
Labarin da aka samu shi ne ana tattaro mutanen kasar Najeriya kusan 2400 da mummunan yakin da ake yi a Sudan ya rutsa da su a yanzu.
Ministocin harkokin waje sun ce gwamnati ta ware $1.2m domin dawo da duka mutanenta gida, motoci 40 su ka bar Khartoum zuwa Masar.
Asali: Legit.ng