Shugaba Buhari Ya Rantsar Da Sabbin Manyan Sakatarori Guda 6
- Sababbin manyan sakatarori guda shida sun yi rantsuwar kama aiki gadan-gadan yau a birnin tarayya Abuja
- Shugaban ƙasa Muhammadu Buhari ne da kansa ya rantsar da sababbin manyan sakatarorin guda shida
- Sababbin sakatarorin sun yi rantsuwar kama aiki ne bayan an kwashe dogon lokaci ana tantance su
Abuja - Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya rantsar da sababbin manyan sakatarori guda shida a ranar Laraba, na ma'aikatun gwamnatin tarayya.
Jaridar Vanguard tace an gudanar da rantsuwar ne a fadar majalisar zartaswa ta fadar shugaban ƙasa da ke Abuja, kafin a fara taron majalisar zartaswa ta ƙasa.
Sababbin manyan sakatarorin da suka kama rantsuwar aiki sun haɗa da Esuabana Nko-Asanye (jihar Cross River), Richard Pheelangwah (jihar Taraba), Mahmud Kambari (jihar Borno), Ibrahim Lamuwa (jihar Gombe), Yakubu Kofar-Mata (jihar Kano) da Oloruntola Michael (jihar Ogun).
Bayanai Sun Fito Daga Tsagin Atiku, Da Yuwuwar Ba Za'a Rantsar da Tinubu a Matsayin Shugaban Ƙasa Ba
A yayin da ya ke karanto jawabin karin sababbin sakatarorin, hadimim shugaban ƙasa na musamman kan harkokin watsa labarai, Femi Adesina, ya ce rantsuwar ta kawo ƙarshen lokacin da aka kwashe ana tankaɗe da rairaya da ofishin shugaban ma'aikatan tarayya ya yi.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
A kalamansa:
"Ya mai girma shugaban ƙasa, mutum shida sun cika sharudɗan zama manyan sakatarori bayan kammala aikin zaɓo su da aka yi wa darektoci kwanan nan.
"Wannan aikin ya ƙunshi gwajin cancanta, da kuma tattaunawa da masu ruwa da tsaki da dama."
Rantsuwar kama aikin na su na zuwa ne ƙasa da wata ɗaya, bayan shugaba Buhari, ya amince da naɗin da aka yi mu su, cewar rahoton Punch.
A ranar 29 ga watan Maris na shekarar 2023, shugabar ma'aikatan gwamnatin tarayya, Dr Folashade Yemi-Esan, ta sanar da cewa shugaban ƙasa ya amince sa naɗin sababbin manyan sakatarori guda shida.
Ana kammala ba sababbin sakatarorin rantsuwar kama aiki, shugaban ƙasa Muhammadu Buhari ya ci gaba da jan ragamar taron majalisar zartaswar ta ƙasa.
Mutum 7 da Buhari Ya Ba Mukami, Kafin a Je Ko Ina Ya Canza Shawara, Ya Sallame Su
A wani rahoton na daban kuma, kun ji yadda wasu mutane bakwai ba su ci moriyar naɗin da shugaba Buhari ya yi mu su ba, a muƙaman da ya ba su.
Mutanen dai bayan an naɗa su ba su daɗewa sosai, sai shugaba Buhari ya sauya shawara, ya sallame su daga aiki.
Asali: Legit.ng