Ma’aurata Da Suka Shafe Shekaru 8 Da Aure Tare Da Yara Sun Gano Su Yan Uwa Ne, Bidiyon Ya Yadu

Ma’aurata Da Suka Shafe Shekaru 8 Da Aure Tare Da Yara Sun Gano Su Yan Uwa Ne, Bidiyon Ya Yadu

  • Wasu ma'aurata da suka shafe shekaru takwas da aure sun haddasa cece-kuce a soshiyal midiya bayan sun gano wani sirri kwanan nan
  • Ma'auratan wadanda Allah ya azurta da haihuwar yara biyu sun gano cewa suna da alaka ta jini kuma matar bata shirya rabuwa da shi ba
  • Jama'a sun yi martani kan bidiyon ma'auratan da ya yadu yayin da suka bayyana ra'ayinsu kan ci gaban

Bayan shafe tsawon shekaru takwas da aure tare da haihuwar yara biyu, wasu ma'aurata sun gano cewa suna da alaka ta jini.

Da take bayyana ci gaban a TikTok, matar, @_purehazel_, ta bayyana cewa su din yan uwa ne kuma kwanan nan suka gano hakan.

Mata da miji da yaransu
Ma’aurata Da Suka Shafe Shekaru 8 Da Aure Tare Da Yara Sun Gano Su Yan Uwa Ne, Bidiyon Ya Yadu Hoto: (_purehazel_)
Asali: TikTok

A wani bidiyo da ya biyo baya inda ta yi martani ga jama'a da ke mamakin dalilin da yasa ya dauke su tsawon shekaru takwas kafin su gano, matar ta ce ba za ta rabu da mijin nata ba, cewa za ta ci gaba da kasancewa da shi. Kalamanta na cewa:

Kara karanta wannan

Matashi Ya Baiwa Mahaifiyarsa Mamaki, Ya Kaita Yawo a Jirgin Sama Don Murnar Zagayowar Ranar Haihuwarta a Bidiyo

"Idan ana rikonka, yana da wahala ka san komai. Don haka idan a karshe ka samu sanin wanene ainahin danginka sannan sai ka ga cewa baka farin ciki da haka.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

"Wannan shine mijina, magana ta kare kuma zan yi bacci a gefensa. Abu daya game da shi, abu biyu tabbass ne, akwai fahimtar juna. Idan aka zo maganar yarana, su ma za su sani, Abu guda da ba zan taba yi ba shine fitar da yarana su san abun da ban sani ba."

Legit.ng ta tuntubi matar don gano yadda ta aka yi ta tabbatar da su yan uwa ne amma har yanzu bata yi martani ba a daidai lokacin kawo wannan rahoton.

Kalli bidiyon a kasa:

Jama'a sun yi martani

Mjabulisi ta ce:

"Wannan bai yi muni ba kasancewarku yan uwa. Hatta a littafin injila iyaye maza sun fadawa yaransu maza da su auri yan uwansu."

Kara karanta wannan

Tir da talauci: An kirkiri motar da mutum zai iya kiranta a waya, kuma ta zo babu direba

Kevin ya ce:

"Toh lokacin yin wani abu ya kure."

SlayedBy Jordan ta ce:

"Sannu da zuwa kudu, Kowa na da alaka ta wani bangare."

Nymeik Gilbert ya ce:

"Wasu abubuwan bai kamata a fade shi ba duk kuna jin dadin bakin baki a wannan dandalin."

Amarya ta zage ta tuka tuwo a wajen shagalin bikinta

A wani labarin, wata amarya ta burge mutane a soshiyal midiya bayan bayyanar bidiyonta tana tuka tuwo katon tukunya a wajen shagalin bikinta.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng