Masu Garkuwa Da Mutanen Sun Bi Dare Sun Yi Awon Gaba Da Mutane Da Dama a Abuja

Masu Garkuwa Da Mutanen Sun Bi Dare Sun Yi Awon Gaba Da Mutane Da Dama a Abuja

  • Masu garkuwa da mutane sun kai farmaki wani ƙauye cikin ƙaramar hukumar Kwali ta birnin tarayya Abuja
  • Miyagun mutanen sun yi awon gaba da mutum 29 waɗanda suka haɗa da matan aure da ƙananan yara
  • Sun kwashe tsawon lokacin a ƙauyen na Yewuti suna cin karen su babu babbakaka suna aikata ta'asa

Abuja - Masu garkuwa da mutane sun yi awon gaba da mutum 29, mazaje, matan aure da ƙananan yara a ƙauyen Yewuti, garin su tsohon mataimakin shugaban ƙaramar hukumar Kwali a birnin tarayya Abuja, Alhaji Zubairu Jibrin Yewuti.

Jaridar Daily Trust ta tattaro cewa matan aure biyu, Zainab Umar da Aisha Zubairu, sun samu sun gudo lokacin da ake tafiya da su cikin daji.

Masu garkuwa da mutane sun sace mutum 29 a Abuja
Masu garkuwa da mutanen sun bi dare wajen aikata wannan ta'asar Hoto: Daily Trust
Asali: Twitter

Wani mazaunin garin wanda ya ɓoye a cikin rufin ɗakin sa, Shuaibu Ndako, ya tabbatar da cewa lamarin ya auku ne da misalin ƙarfe 1 na dare ranar Talata a lokacin da gungun masu garkuwa da mutanen suka dira cikin ƙauyen.

Kara karanta wannan

An Samu Karin Wasu 'Yan Matan Chibok Da Suka Tsero Daga Hannun Boko Haram

Ya bayyana sun raba kan su kashi-kashi sannan suka shiga gidaje 8 yayin da suke ta harba bindiga, inda suka riƙa ɗaukar mutane ciki har da ƙananan yara da matan aure suna tafiya da su daji.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Mataimakin ƙaramar hukumar Abaji wanda ya sauka, Alhaji Zubairu Jibrin Yewuti, ya ce ƙanin sa Idris da wasu matan yayyen sa guda biyu da wani ƙaramin yaro na daga waɗanda aka ɗauke a gidan su.

Ya bayyana cewa ƴan bindigan waɗanda suka ci karen su babu babbaka tun daga ƙarfe 1 na dare har zuwa 3 na dare, sun shiga gidaje takwas, sannan suka ɗauki mutum 29 , waɗanda suka haɗa da mata, mazaje da ƙananan yara.

Mai girma Etsu Abawa na Yewuti, Alhaji Isyaku Yakubu Yewuti, ya ƙara tabbatar da cewa an sace mutum 29 daga cikin mutanen sa, cewar rahoton Within Nigeria.

Kara karanta wannan

Masha Allah An Fara Jigilar 'Yan Najeriya Da Suka Makale a Sudan, Yau Za a Kwaso Da Dama

Ya ce mutum biyu da suka samu raunika an kai su wani asibitin kuɗi a Kwali.

Basaraken wanda ya bayyana cewa gabaɗaya mutanen ƙauyen sun gigita saboda harbin bindigan masu garkuwa da mutanen, ya yi kira ga jami'an tsaro da su kawo mu su ɗauki wajen ceto mutanen da aka sace.

Wasu Karin 'Yan Matan Chibok Sun Tsero Daga Hannun Boko Haram

A wani rahoton kuma, kun ji yadda wasu ƴan matan Chibok suka samu nasarar gudowa daga hannun mayaƙan ƙungiyar Boko Haram.

Ƴan matan guda biyu, sun dai kwashe tsawon shekara 9 a hannun Boko Haram tun bayan da aka sace su a shekarar 2014.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng