Hukumar EFCC Ta Gurfanar da Kakakin Majalisar Ondo da Wasu Jiga-Jigan Siyasa 2
- Hukumar EFCC ta gurfanar da wasu manyan ‘yan siyasa a jihar Ondo da ke Kudu maso Yammacin Najeriya
- Ana zargin kakakin majalisa da wasu jiga-jigai biyu a jihar da aikata zamba, amma sun musanta zargin
- Ya zuwa yanzu, an ba da belinsu, amma za a sake gurfanar dasu a gaban kotun a ranar 18 ga watan Mayu
Jihar Ondo - Hukumar zaki da cin hanci da rashawa a Najeriya (EFCC) a ranar Talata 25 Afirilu, 2023 ta gurfanar da kakakin majalisar jihar Ondo, Rt. Hon. Bamidele Oloyeloogun a gaban babban kotun Akure bisa zargin aikata zamba.
Hakazalika, an gurfanar da wani dan majalisar jiha mai wakiltar mazabar Akoko South/West 1, Felemu Bankole da kuma wnai ma’aikacin gwamna, Segun Oyadeyi Bankole.
Wadanda ake zargin gaba daya sun musanta zargin da ake musu na aikata zamba, kamar yadda Channels Tv ta ruwaito.
A jefa su a magarkama kawai
Lauyan hukumar EFCC, Kingsley Kudus ya nemi kotun da ta garkame wadanda ake zargin a gidan gyaran hali na Olokuta a birnin Akure.
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
Ya yi turjiya da cewa, duk da sun musanta zargin da ake musu, suna hannun kotun ne sai yadda ta yi dasu wajen tantance gaskiyarsu ko akasin haka.
Lauyan wadanda ake zargin, Barista Femi Emodamori ya shaidawa kotun cewa, yana shirya tsaf don ci gaba da sauraran kara da hujjoji a gaban kotun, Vanguard ta ruwaito.
Ya kuma nemi kotun da ta yi watsi da bukatar EFCC na tsare wadanda yake karewa, inda yace suna da damar samun beli a halin da ake ciki.
Kakakin majalisa na da laurarar rashin lafiya
Ya yi bayanin cewa, wanda ake zargi na biyu (Oleyeloogun) na da larura ta rashin lafiya da ke bukatar kulawar gaggawa.
Ya kuma roki kotun da ta gargadi daya daga wadanda ke korafi game da lamarin, wato tsohon kakakin majalisar Ondo Hon. Iroju Ogundeji da ke tura sako mara dadi ga Oleyeloogun.
A cewar lauyan, matukar Ogundeji bai daina tura sakon ba to tabbas za su maka shi a gaban kotu don daukar mataki a kansa.
A hukuncinsa, mai shari’a Adegboyega Adebusoye ya ba da belin wadanda ake karan ya har zuwa lokacin da kotun zai sake zama, wanda daga nan ya dage ci gaba da sauraran karar zuwa ranar 18 ga watan Mayun 2023.
EFCC t sha bayyana irin satar da 'yan siyasa ke yi, inda tace da yawan gidajen da ake gani a Abuja da Legas mallakin barayin gwamnati ne.
Asali: Legit.ng