Arewacin Najeriya Zai Samu Gas da Lantarki, An Yi 70% na Aikin AKK Inji NNPCL
- Mele Kolo Kyari ya tabbatar da aikin da ake yi na AKK a yankin Arewacin Najeriya yana tafiya
- Bayanin Shugaban kamfanin NNPCL ya karyata rade-radin da ke yawo na tsayawar kwangilar
- A cikin $2.8bn da za a kashe a wajen shimfida bututun mai daga Abuja zuwa Kano, an fitar da $1.1bn
Abuja - Shugaban kamfanin mai na kasa watau NNPCL, Mele Kolo Kyari ya samu damar yin bayanin inda aka kwana a aikin shimifida gas na AKK.
A wata sanarwa da ta fito daga shafin NNPCL na Twitter, an fahimci kwangilar AKK da aka dauko daga Ajaokuta zuwa Kano, ya yi nisa sosai a halin yanzu.
Da ya kai ziyara zuwa garin Ahoko a jihar Kogi domin ganin yadda abubuwa suke tafiya, Malam Mele Kolo Kyari ya tabbatar da cewa an kai 70% na aikin.
29 Ga Watan Mayu: Fitattun Yan Najeriya 5 Da Ake Ganin Su Buhari Ke Baiwa Hakuri a Sakonsa Na Barka Da Sallah
Shugaban na NNPCL ya ce an batar da Dala biliyan 1.1 a kan wannan aiki da zai kawo gas.
Za a samu wuta a Abuja-Kaduna-Kano
Mele Kyari yake cewa aikin zai ci Dala biliyan 2.8, kuma idan an kammala komai zai taimakawa tashohin wutar Najeriya da karfin lantarki megawatt 3650.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Tribune ta ce Kyari da ‘yan tawagarsa sun ziyarci Ahoko a ranar Litinin, yake cewa duk da rashin samun kudi daga ragowar bangaren, aikin ya na ta tafiya.
Jawabin Mele Kolo Kyari
“Yana da matukar kima ga Najeriya da cigaban tattalin arziki da zamantakewarta. Aikin bai tsaya ba ko da na kwana guda.
Mun cigaba da narka kudi duk da babu inda ake samun wasu kudin daga sauran bangarori.
Yanzu da muke magana, babu ‘dan kwangilar da yake bin mu bashin sisin kobo. Mun biya duka kudin ayyukan da aka yi mana.
Akwai wurare fiye da 30 da aikin nan yake gudana, kuma mu na sa rai za mu kammala kwangilar nan.
- Mele Kolo Kyari
Rahoton ya nuna Kyari ya ce bututun da za a shimfida za su iya takun kubic biliyan biyu na gas a duk rana zuwa tashohin da ke Abuja, Kaduna da Kano.
Shugaban na NNPPCL yake cewa an kera 94% na bututun da ake bukata, baya ga haka, 90% sun iso Najeriya, game da batun shimfida su kuwa, an yi nisa.
An kara 40% a albashi
Kamar yadda rahoto ya zo, an yi wa kowa karin albashi saboda shirin janye tallafin man fetur, amma ma’aikatan jami’o’in gwamnati ba su san ana yi ba.
Malamai da sauran ma’aikatan jami’a su na zargin ana yi wa harkar ilmi rikon sakainar kashi. Ministan kwadago ya nuna ba a manta da su a karin ba.
Asali: Legit.ng