Tashin Hankali Yayin da Aka Binne Wani Tsoho da Ransa Saboda Zarginsa Da ‘Maita’ a Benue

Tashin Hankali Yayin da Aka Binne Wani Tsoho da Ransa Saboda Zarginsa Da ‘Maita’ a Benue

  • Wasu fusatattun matasa sun mangare tsoho tare da binne shi da ransa a wani yankin jihar Benue a Arewacin Najeriya
  • Wannan lamarin ya faru ne sakamakon zargin da matasan suka yi na cewa tsohon ya kashe mutane uku ta hanyar maita
  • Rundunar ‘yan sanda ta tabbatar da faruwar lamarin, ta kuma bayyana kame wasu da ake zargin da su aka kashe wannan tsohon

Jihar Benue - Wani tsoho ya gamu da tasgaro yayin da aka binne shi da ransa bisa zargin yana mummunar dabi’ar maita a garin Ikyve da ke karamar hukumar Konshisha ta jihar Benue.

Wani ganau ya bayyana cewa, lamarin ya faru ne a karshen mako a yankina na Ikyve da ke Diiv-Ikyurave, wani kauye da ke da iyaka da jihar Kuros Riba.

Wani mazaunin yankin ya yi bayani da cewa, rikicin ya faru ne da tsohon suna Ihwakaa yayin da tsawa ta kashe dansa Henry da kuma matarsa da dan jaririn dansu.

Kara karanta wannan

Tir da talauci: An kirkiri motar da mutum zai iya kiranta a waya, kuma ta zo babu direba

Yadda aka kama matasan da suka hallaka tsoho a Benue
Jihar Benue da ke Arewa ta Tsakiyar Najeriya | Hoto: thenationonlineng.net
Asali: UGC

Ana zargin tsoho ya kashe ahalinsa ta sanadiyyar maita

Daga baya, matasan garin sun yi zargin cewa, tsawar ta kashe dangin tsohon ne ta sanadiyyar maitarsa, wanda suka ce yana amfani da ruwan sama wajen cimma nufinsa na maita.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

A cewar mazaunin yankin:

“Saboda haka, suka farmake shi kana suka binne shi a wani rami mara zurfi da ransa.”

Wani mazaunin yankin mai suna Engr. Baba Agan ya shaidawa Daily Trust cewa, tabbas ya samu labarin mutuwar wasu mutum uku ta sanadiyyar tsawa a garin.

Agan ya ba da lamarin cewa, daga baya ne ya samu labarin cewa ana zargin tsohon da hannu a mutuwar mutanen uku, lamarin da ya kai ga fusatattun matasa suka binne shi da ransa.

Ya ce, tsawa dai abu ne da an saba dashi kuma ba mutum ne mai kawo ba, don haka bai kamata a zargi tsohon da aikata kisan mutum uku ba.

Kara karanta wannan

Wani Bawan Allah Ya Mutu A Hanyarsa Ta Dawowa Daga Masallaci A Ranar Sallar Idi

Abin takaici, tsoho ya mutu a karamin rami

Agan, wanda shi ma wani shugaba ne a yankin ya yi Allah wadai da lamarin, inda yace abin takaici kafin ‘yan sanda su zo ceto tsohon, tuni ya mutu sai kawai suka ciro gawarsa.

Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Benue, SP Catherine Anene ta tabbatar da faruwar lamarin, inda tace an kama wasu mutum biyu da ake zargin suna da hannu a kisan tsohon, rahoton Daily Sun.ta tattaro.

A wani labarin, kunji yadda wani gini ya ruguje kan wasu mutane, inda ake fargabar ya kashe mutane tare da jikkata da yawa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.