Sojoji Sun Yi Kaca-Kaca da Maboyar ’Yan Bindiga a Zamfara, Sun Kashe da Yawa, Sun Kama Wasu
- Rahoton da muke samu ya bayyana yadda sojojin Najeriya suka yi nasarar fatattakar ‘yan ta’adda a jihar Zamfara
- An hallaka ‘yan bindiga bakwai tare da kwato kayayyakin aikata barna masu yawa a hannun masu tada hankalin jama’a
- Hakazalika, an kama wasu ‘yan bindiga tare da kamo wanda kasurgumin da ke kai musu bayanan sirri game da jama’ar gari
Jihar Zamfara - Rundunar sojin Najeriya karkashin tawagar Operation Hadarin Daji sun yi fata-fata da ‘yan bindiga bakwai tare da lalata mafakarsu da yawa da kuma kwace babura bakwai a karamar hukumar Shinkafi ta jihar Zamfara.
Wannan bayani na kunshe ne a cikin wata sanarwar da daraktan yada labarai na hedkwatar tsaron Najeriya da ke Abuja, Manjo Janar Musa Danmadami, rahoton Punch.
Danmadami ya ce, jami’an tsaron sun kuma kwato mujallun AK-47 guda biyu da kuma na’urar sadarwa ta Baofeng.
An kama ‘yan ta’adda bayan sheke wasu
A cewar wani yanki na sanarwar kamar yadda Daily Post ta tattaro.
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
“Biyo bayan kama wani mai kai wa ‘yan ta’adda bayanan sirri a ranar 21 ga watan Afrilu, jami’ai sun yi aikin bin kafa tare da kama ‘yan ta’adda biyu a ranar 22 ga watan Maris a garin Shinkafi da ke karamar hukumar Shinkafi ta jihar Zamfara.
“Kayayyakin da aka kwato daga wadanda ake zargin sun hada da babur daya da wayoyin hannu guda uku.”
“Babban kwamandan soji ya yada da kokarin jami’an Operation HADARIN DAJI kana ya karfafa gwiwar al’umma da su ci gaba da ba jami’ai bayanai masu muhimmanci akan lokaci game da ayyukan ‘yan ta’adda.”
Jami’an tsaro na ci gaba da samun nasara kan ‘yan ta’adda a bangarori daban-daban na Najeriya a irin wannan lokacin.
An sace direban mataimakin gwamnan jihar Nasarawa
A wani labarin kuma, kunji yadda wasu tsagerun ‘yan bindiga suka sace direban mataimakin gwamnan jihar Nasarawa da ke Arewa ta Tsakiya a Najeriya.
Wannan lamarin ya faru ne a lokacin da ya ziyarci abokinsa da dare, inda aka sace shi aka barshi da motarsa a hanya.
Ya zuwa yanzu, an tabbatar da sace mutumin, amma ba a bayyana abin da suke nema ba, duk da cewa har yanzu jami’an ‘yan sanda na ci gaba da neman inda aka kai shi.
Asali: Legit.ng