Mutum 5 Sun Rasu A Hadarin Jirgin Ruwa A Kano, An Ceto Wasu Shida Da Ransu
- Mutane a Jihar Kano sun shiga jimamin rashin yan uwansu da suka rasu sakamakon wani hadarin jirgin ruwa da ya faru a ranar Lahadi 23 ga watan Afrilu
- Kamar yadda hukumar kashe gobara ta jihar Kano ta tabbatar, an rasa rayyuka guda 5 sannan an ceto fasinjoji shida daga cikin jirgin ruwan bayan afkuwar lamarin a karamar hukumar Madobi
- Alhaji Saminu Abdullahi, jami'in hulda da jama'a na hukumar kashe gobara ta Kano ya ce an fara bincike kan afkuwar hadarin jirgin ruwan kuma za a sanar da sakamakon binciken daga bisani
Jihar Kano - Hukumar Kashe Gobara ta Jihar Kano a ranar Lahadi ta tabbatar da mutuwar wasu mutane biyar yayin da mutane shida suka tsira sakamakon hadarin jirgin ruwa a Dam din Kanwa da ke karamar hukumar Madobi na jihar.
Mai magana da yawun hukumar, Alhaji Saminu Abdullahi, ya fada wa Kamfanin Dillancin Labarai na Kasa a wayar tarho a Kano cewa wani Umar Faruk-Dalada, ya kai musu rahoton afkuwar lamarin da inda ya faru, The Punch ta rahoto.
Ya ce:
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
"Lamarin ya faru a ranar 22 ga watan Afrilu, misalin karfe 5.40 na yamma."
"Akwai kimanin mutane 11 a cikin jirgin ruwan, an ceto shida da ransu yayin da guda biyar an ceto su ba su numfashi."
Sunayen Mutanen Da Suka Rasu A Hadarin Jirgin Ruwa a Kano
Ya lissafa sunayen wadanda suka rasa rayyukansu kamar haka:
- Abdulrazak Nabara dan shekara 40
- Dalha Muktar-Atamma dan shekara 40
- Mustapha Ibrahim, dan shekara 45
- Umar Isah dan shekara 35, da
- Umar Idris dan shekara 35.
Mai magana da yawun hukumar ya ce wadanda abin ya ritsa da su sun fito ne daga karamar hukumar Fagge na jihar, Daily Trust ta rahoto.
Ya ce an fara bincike dangane da hatsarin jirgin ruwan kuma za a sanar da rahoton abin da aka gano bayan an kammala binciken.
Mutane Da Dama Sun Riga Mu Gidan Gaskiya Sakamakon Hadarin Jirgin Ruwa A Kano
A wani rahoton a baya kun ji cewa mutane biyu sun riga mu gidan gaskiya sakamakon hadarin jirgin ruwa da ya faru a kauyen Zangon Durgu da ke karamar hukumar Rimin Gado a jihar Kano.
Saminu Yusuf Abdullahi, mai magana da yawun hukumar kashe gobara ta jihar Kano ne ya tabbbatarwa yan jarida afkuwar lamarin kamar yadda jaridar Daily Trust ta rahoto.
A cewarsa, jirgin ruwan ya dako mutane hudu ne kacal yayin da ya kife a kan hanyarsa ta zuwa garin Kanya daga kauyen Zangon Durgu.
Asali: Legit.ng