Babbar Magana Yayin da DSS Suka Kama Bindigogi Boye a Cikin Buhunnan Doya a Kano
- Hukumar tsaro ta farin kaya ta kame wasu bata-garin da suka shigo da makamai cikin jihar Kano da ke Arew maso Yamma
- An ruwaito cewa, jami’an sun kama mutanen ne a lokacin da suka boye bindigogin a cikin buhunnan doya a jihar
- A halin yanzu, an ba mutane shawari game da bukukuwan sallah da kuma yadda za a kula da sanya ido kan motsin jama’a
Jihar Kano - Hukumar tsaro ta farin kaya (DSS) a ranar Alhamis ta kame wasu bindigogi da aka boye a buhunnan doya a jihar Kano, ta kwamushe mutum biyu da ake zargi.
Ana zargin mutanen da dauko bindigogin ne daga wani wuri, ana kuma kyautata zaton za su wuce dasu wasu jihohin Arewa ne don aikata barna dasu, Daily Trust ta ruwaito.
Kakakin hukumar DSS, Peter Afunanya ne ya bayyana hakan ga manema labarai a Abuja, inda yace an kama bindigogi AK-47 guda biyu da mujallu biyu na AK-47 da babu komai a cikinsu.
A cewar Afunanya, an kuma kama buhunnan doya da wata babur mai launin ja duk dai wadanda aka boye kayan aikata laifin a cikinsu.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Ya kamata kowa ya kula
A bayaninsa, ya yi kira ga masu gidajen shakatawa da wuraren wasanni da su kula sosai a lokacin bukukuwan karamar sallah da ake fuskanta, rahoton Daily Post.
A cewarsa:
“Wannan lamarin ya nuna akwai bukatar ‘yan kasa su zuba ido sosai kuma kai rahoton duk wani bakon abu ko motsin abin zargi, mutum ko su dauki matakin kai batun ga cibiyoyin tsaro mafi kusa.
“Masu gidajen shakatawa, gidajen saukar baki da bude ido duk ana shawartarsu da su kula a lokacin bukukuwa.
“Ya kamata su dauki matakan kariya a wurarensu. Sai dai, hukumar na yiwa Musulmai fatan bikin karamar sallah cikin lumana da farin ciki.”
Hakazalika, hukumar ta ce za ta yi aiki kafada da kafada da sauran hukumomin tsaro don tabbatar da zaman lafiya da kwanciyar hankali a kasar nan.
Soja ya kashe dan sanda saboda tabar wiwi a Borno
A wani labarin kuma, kunji yadda wani jami’in soja ya hallaka dan sanda a jihar Borno saboda rikicin da ya barke don an kama su da tabar wiwi.
An ruwaito cewa, an kama sojan ne a cikin motarsa lokacin da ya dauko tulin tabar wiwi don shiga da shi wani yankin jihar.
Ya zuwa yanzu, ana ci gaba da bincike don gano tushen lamarin da kuma yiwuwar daukar matakin da ya dace.
Asali: Legit.ng