Shugaba Buhari Ya Kori Kwamishinan INEC Din da Ya Dagula Zaben Jihar Adamawa

Shugaba Buhari Ya Kori Kwamishinan INEC Din da Ya Dagula Zaben Jihar Adamawa

  • Shugaba Buhari ya umarci a yi bincike kan Hudu Yunusa Ari, kwamishinan zaben jihar Adamawa kan batun da ya shafi zaben jihar
  • Hudu ya jawo cece-kuce a lokacin da ya sanar da sakamakon zaben jihar Adamawa duk da kuwa ba huruminsa bane
  • Ya zuwa yanzu, za a dauki mataki kan Hudu idan aka gano yana da laifi, kuma shugaba Buhari ya sanya hannu kan hakan

FCT, Abuja - Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya amince da koran kwamishinan zaben jihar Adamawa, Mr Hudu Yunusa Ari, jaridar Punch ta ruwaito.

Dakatar da Hudu zai ci gaba da kasancewa ne har zuwa lokacin da sufeta janar na ‘yan sandan Najeriya, Usman Baba zai kammala bincike game da kitimurmurar da ta faru a zaben jihar Adamawa na cike gurbi.

Hakazalika, a nan take Buhari ya umarci sufeto janar na ‘yan sandan da ya fara bincike da hukunta Hudu idan aka kama shi da laifi.

Kara karanta wannan

Zaben Adamawa: Zababben Shugaban kasa, Tinubu ya yi kira ga ‘Yan Sanda da Binani

Buhari ya dakatar da Hudu Ari
Shugaban kasa Muhammadu Buhari | Hoto: premiumtimesng.com
Asali: UGC

Idan baku manta ba, Hudu ya birkita zaman lafiyar zaben jihar Adamawa a ranar Lahadin da ta gabata, inda ya sanar da zabe duk da kuwa ba shi ya kamata ya yi hakan ba.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Sanar da dakatar da Hudu

Wannan mataki na Buhari na fitowa ne da ofishin sakataren gidan gwamnatin tarayya ta hannun daraktan yada labaran ofishin, Willie Bassey.

Sanarwar ta yi ishara ga sauran hukumomin tsaron Najeriya da su gudanar da bincike don daukar matakin da ya dace kan kwamishinan, rahoton DailyPost.

A bangare guda, kunji yadda aka samu tsaiko a lokacin da Hudu Ari ya yi riga malam masallaci, ya sanar da sakamakon zaben jihar Adamawa duk da kuwa ba huruminsa bane.

Yadda zaben Adamawa ya zo da tsaiko

Rahotanni sun bayyana cewa, Hudu ya ayyana Aisha Binani a matsayin wacce ta lashe zaben gwamnan jihar Adamawa da ke Arewa maso Gabashin Najeriya.

Kara karanta wannan

Abin da Ya Hana Buhari Tsoma Baki a Tirka-Tirkar Binani da Fintiri – Gwamnatin Tarayya

Bayan haka ne hukumar zabe mai zaman kanta ta dakatar da ci gaba da tattara sakamakon zaben cike gurbin da aka gudanar a ranar Asabar din da ta gabata.

Ya zuwa yanzu, hukumar zabe ta INEC ta bayyana cewa, Ahmad Fintiri ne lashe zaben gwamnan jihar Adamawa, kuma ya yi nasara da kuri’un da suka taka na Binani.

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.