Wata Matar Aure Ta Ci Tarar Mijinta 57k Saboda Ya Dawo Gida a Makare

Wata Matar Aure Ta Ci Tarar Mijinta 57k Saboda Ya Dawo Gida a Makare

  • Wasu ma'aurata da ke cikin farin ciki sun wallafa bidiyon yadda matar ta hana sahibinta shiga gida
  • A cikin bidiyon mai ban dariya, matar ta matsa dole mijin ya biya tarar N57,249 saboda ya koma gida a makare kuma ya karya dokar gidan
  • Da yawan mutanen da suka kalli bidiyon sun ce mutumin ya ɗan ji kunya duk ya nemi a rage masa kuɗin tarar zuwa rabi

Wata zankaɗediyar Amarya (@jessicaseth) da matashin Angonta, wanda suka saba kirkirar kyawawan abubuwa game rayuwar gidansu a TikTok, sun saki sabon bidiyo.

A ɗan gajerin bidiyon na TikTok, ma'auratan sun nuna cewa kowa ya ɗauki abokin zamansa a matsayin babban aboki. Matar ta tsaya bakin ƙofa ta hana mijinta shiga cikin gida.

Ma'aurata.
Wata Matar Aure Ta Ci Tarar Mijinta 57k Saboda Ya Dawo Gida a Makare Hoto: @jessicaseth
Asali: TikTok

Ta zargi mai gidanta da dawo wa gida a makare daga wurin aikinsa, ta ce ya ƙara awanni biyu daga lokacin da ya kamata a ce ya dawo gida.

Kara karanta wannan

Abin Al'ajabi a Najeriya: Wani Bawan Allah Ya Sha Mamakin Kuɗin Da Ya Samu Bayan Ya Roki Allah $100m

Mutumin ya yi koƙarin sulhu da matarsa

Matar ta ce sakamakon wannan laifin da ya aikata, ya saɓa wa doka mai lamba ɗaya da suka gindaya a gidansu. Don haka ta buƙaci Mijin ya biya £100 (N57,249.08) kafin ta iya barinsa ya shiga gida.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Magidancin, wanda ya nuna jin kunya kan hukuncin da matarsa ta yanke masa, ya roki ta taimaka ta rage masa kudin su dawo £50 (N28,629.60).

Da yawan mutanen da suka kalli bidiyon sun nuna cewa ma'auratan suna gina gida mai kyau. Bidiyon ma'auratan ya tara ra'ayoyin jama'a aƙalla 1,700.

Bidiyon yadda aka yi dirama tsakanin ma'auratan

Legit.ng Hausa ta tattara muku wasu ra'ayoyin mutane game da wannan bidiyo.

Maryann ta ce:

"Shin mijin naki shi kaɗai ne?"

Ama Konadu ta ce:

"Dan Allah yar uwa a wace manhaja kika ɗauko shi? Ki taimaka yar uwata, ciwon 'ya mace na 'ya mace ne ko ba haka ba."

Kara karanta wannan

Karin Bayani: An Rasa Rayuka Yayin da Wani Gini Ya Tumurmushe Mutane a Abuja Cikin Azumi

Shaggy ya ce:

"Amma mutumin kirki ne kuma mai kunya."

A wani labarin kuma Wani Mutumi Ya Roki Allah Dala Miliyan $100m, Nan Take Allah ya karbi addu'arsa a bidiyo

Musulmai sun yarda da Addu'a musamman a lokacin watan Azumin Ramadana, akwai lokuta da yawa wadanda idan ka yi Addu'a Allah zai karɓa.

Wani bawan Allah ya ga abin Al'ajabi kwana biyu bayan ya kai kokensa wurin Allah SWT, ya samu makudan kuɗi.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262