Ana Dab Da Rantsar Da Tinubu, Nasir El-Rufa'i Ya Hango Wata Babbar Matsala

Ana Dab Da Rantsar Da Tinubu, Nasir El-Rufa'i Ya Hango Wata Babbar Matsala

  • Gwamnan jihar Kaduna ya koka kan matsalar rashin tsaro yayin da ake tunkarar mika mulki ga zaɓaɓɓen shugaban ƙasa a ranar Litinin, 29 ga. watan Mayun 2023
  • Gwamna Nasir El-Rufai ya buƙaci gwamnatin tarayya ta ƙara tsaurara tsaro a faɗin ƙasar nan saboda ƴan bindiga za su iya amfani da lokacin su kai munanan hare-hare
  • El-Rufai ya bayyana hakan ne a wajen gabatar da rahoton tsaro na gwamnatin jihar Kaduna a babban birnin jihar ranar Laraba, 19 ga watan Afirilu

Jihar Kaduna - Gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufai, ya janyo hankali kan matsalar tsaro da ake fama da ita a ƙasar nan, yayin da ake tunkarar bikin murnar rantsar da zaɓaɓɓen shugaban ƙasa, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu.

El-Rufai ya bukaci a kara tsaurara matakan tsaro
El-Rufai ya nemi shugaba Buhari ya kara tsaurara matakan tsaro kafin rantsar da Tinubu Hoto: Nasir El-Rufai, Muhammadu Buhari, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu
Asali: Facebook

Zaɓaɓɓen shugaban ƙasar na Najeriya zai hau kujerar iko kan madafun ƙasar nan ne a ranar 29 ga watan Mayun 2023.

Kara karanta wannan

Gwamnatin Tarayya Ta Yi Wa Shugaban Wata Babbar Hukuma Ritayar Dole, Ta Bayar Da Dalilai

Jaridar Punch ta tattaro rahoto cewa, gwamna El-Rufai yayi gargaɗin cewa ƴan bindiga na iya amfani da lokacin miƙa mulkin su ƙaddamar da munanan hare-hare a ƙasar nan.

Gwamnan ya bayar da shawarar yakamata a ƙara matsa kaimin da ake yi na ganin an murƙushe ƴan bindiga a kwanakin da suka rage na wannan gwamnatin da bayan wucewar ta.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Nasir El-Rufai ya bayyana hakan ne a wajen gabatar da rahoton tsaro na kwamishinan tsaro da harkokin cikin gida, Samuel Aruwan, a gidan gwamnatin jihar na Sir Kashim Ibrahim, a Kaduna babban birnin jihar ranar Laraba.

Gwamnan ya yi kira da a cigaba da luguden wuta ta sama da ƙasa da ake a yankin Arewa maso Yamma, wanda yake fama da matsalar tsaron da ta ƙi ci ta ƙi cinyewa.

A kalamansa:

Muna roƙon da a ci gaba da luguden wuta a ragowar kwanakin da suka ragewa wannan gwamnatin da bayan wucewar ta, ta yadda sauyin gwamnati a matakin tarayya, ba zai sanya a samu giɓin da ɓata gari za su yi amfani da shi ba."

Kara karanta wannan

Bayan Lallasa Dan Majalisa Mai Ci a Zabe, Matashin Dan Majalisa Ya Bayyana Inda Ya Samo Kudin Kamfe

Sarkin Musulmi Ya Nemi 'Yan Najeriya Su Yi Addu'o'i

A wani rahoton na daban kuma, kun ji yadda sarkin musulmi ya buƙaci ƴan Najeriya da su yi addu'o'in samun nasarar miƙa mulki ga sabuwar gwamnati.

Alhaji Sa'ad Abubakar III ya kuma nemi sababbin shugabanni da su sanya tsoron Allah a zukatan su wajen gudanar da mulkin su.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng