Ana Dab Da Sallah, Sarkin Musulmi Ya Aike Da Wani Muhimmin Sako Ga Al'ummar Najeriya

Ana Dab Da Sallah, Sarkin Musulmi Ya Aike Da Wani Muhimmin Sako Ga Al'ummar Najeriya

  • Sarkin musulmi ya buƙaci ƴan Najeriya da su yi addu'o'in samun nasarar miƙa mulki ga sabuwar gwamnati
  • Aƙhaji Sa'ad Abubakar III ya kuma yi fatan gwamnati mai ci ta kammala wa'adin ta cikin nasara
  • Sarkin musulmin ya kuma yi kira ga gwamnatoci masu zuwa da su sanya tsoton Allah a zukatan su wajen gudanar da mulkin su

Jihar Kaduna - Sarkin musulmi, Alhaji Muhammadu Sa’ad Abubakar, a ranar Laraba ya yi kira ga ƴan Najeriya da su yi addu'ar miƙa mulki ga sabuwar gwamnati cikin lumana a faɗin ƙasar nan.

Jaridar Vanguard tace Sarkin musulmin ya yi wannan kiran a wata sanarwa da babban sakataren ƙungiyar Jama’atu Nasir Islam (JNI), Dr Khalid Aliyu, ya fitar a Kaduna.

Sarkin musulmi ya bukaci 'yan Najeriya su yi addu'o'i
Sarkin musulmi ya yi muhimmin kira ga 'yan Najeriya. Hoto: Vanguard.com
Asali: UGC

Sarkin musulmin kuma shugaban JNI, ya kuma yi fatan ƙarewar wa'adin gwamnatin shugaban ƙasa Muhammadu Buhari cikin kwanciyar hankali.

Kara karanta wannan

Karin Bayani: An Rasa Rayuka Yayin da Wani Gini Ya Tumurmushe Mutane a Abuja Cikin Azumi

Ya yi ga gwamnatocin da za su karɓi madafun iko da su yi gaskiya, adalci da kuma buɗe kunnuwan su, musamman kan lamuran tsaro da kuma tsoron Allah wajen gudanar da mulkin su.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

A kalamansa:

"Dukkanin mu za mu amsa tambaya kan abubuwan da mu ka aikata a gaban Allah, hakan yakamata ya zama izna a gare mu ya sanya mu shiga taitayin mu."

Sarkin musulmi ya taya musulmai zuwan Sallah

Sarkin musulmin ya ce JNI na miƙa saƙon taya murnarta ga musulman duniya busa kammala azumin watan Ramadan da zuwan sallar Eid-el-Fitr, cewar rahoton Gazettengr.

A cewarsa:

"Allah ya sanya wannan lokacin murnar ya zama lokacin farin ciki, zaman lafiya da albarka ga dukkan musulmai da iyalan mu da kuma makusantan mu."
"Muna roƙon Allah maɗaukakin sarki ya amsa mana dukkanin addu'o'in mu, azumin mu da ayyukan alkhairin mu na lokacin Ramadan, sannan ya ci gaba da lulluɓe mu da Rahamar Sa a kwanaki da watanni masu zuwa."

Kara karanta wannan

Karin Bayani: Mai Alfarma Sarkin Musulmi Ya Fitar da Sanarwa Mai Muhimmanci Ana Gab Da Sallah

Sarkin Musulmi Ya Taya Zababben Gwamnan Sokoto Murna

A wani rahoton na daban kuma, kun ji yadda Sarkin musulmi ya aike da saƙon taya murnar sa ga zaɓaɓɓen gwamnan jihar Sokoto.

A saƙon taya murnar da ya aikewa Alhaji Ahmed Aliyu, Sarkin musulmin ya nuna a matsayin sa na uba a shirye yake ya bayar da duk irin gudunmawar da ta dace wajen ciyar da jihar gaba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng