Alkali Ya Maido Wanda Shugaban kasa Ya Kora Daga NNPCL, Kotu Ta ce a Biya Shi N5bn
- Babban kotun tarayya ta Abuja ta ba Ifeanyi Ararume gaskiya a shari’arsa da gwamnati
- Gwamnati ta tsige Ararume daga matsayin Darekta a NNPCL kafin a kai ga rantsar da shi a ofis
- ‘Dan siyasar ya fadawa an saba doka da aka tunbuke shi, kotu ta gamsu da karasa, ta gaskata shi
Abuja - Babban kotun tarayya mai zama a garin Abuja, ta ce korar Ifeanyi Ararume daga kujerar Darekta mara iko a kamfanin NNPCL ya saba doka.
Rahoton Premium Times ya ce sallamar Ifeanyi Ararume da aka yi ta ci karo da dokar kasa, a dalilin haka Inyang Ekwo, ya dawo da shi mukaminsa.
Bayan dawo da shi kan kujerarsa, Mai shari’a Inyang Ekwo ya umarci gwamnatin tarayya ta biya shi duk hakkokin Darekta a kamfanin man kasar.
Alkalin ya kuma soke duk matakan da majalisar da ke kula da NNPCL ta dauka bayan sauke Ararume, sannan aka bukaci a biya shi Naira biliyan 5.
Ba a bi dokar CAMA ba
Ganin wasika ta SGF. 3V111/86 da Sakataren gwamnati ya aiko masa, Ararume ya shigar da kara a kotu bisa zargin an saba dokar CAMA wajen tsige shi.
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
A karar da ya shigar, tsohon Darektan na NNPCL ya bukaci a biya shi Naira biliyan 100 domin ya rage zafi a kan tuntubuke shi da aka yi ba kan ka’ida ba.
A karshen 2021 aka nada shi a matsayin Darekta da zai yi shekara biyar, amma sai ga shi an kore shi a Junairun 2022, ko rantsar da shi ba a kai ga yi ba.
Sai kwanaki goma bayan an rantsar da wani dabam a kujerar da yake tunanin shi zai dare, sai Ararume ya ga takarda, ana sanar da shi cewa an sauke shi.
"Shugaban kasa bai da ikon sauke ni" - Ararume
A karar da ya shigar, tsohon ‘dan takaran gwamnan ya ce shugaban kasa bai da ikon da zai tunbuke shi domin NNPCL ya zama kamfani da ke aiki da CAMA.
Kamar yadda dokar PIA ta 2021 ta ce, tun da ba a same shi da aikata wani laifi da ya cancanci rasa kujerar Darekta ba, Ararume ya ce ba za a iya korar shi ba.
A cewarsa, matakin da aka dauka ya saba sashe na 63 (3) na dokar PIA ganin bai mutu ba, kuma ba murubus ya yi ba, Vanguard ta ce za a daukaka karar.
Taron shan ruwa a Saudi
An ji labari wasu Sarakunan kasar nan, Shugaban kungiyar Izala, Limaman babban masallacin Abuja da na Aso Rock sun sha ruwa da shugaban kasa.
Alhaji Aminu Ado Bayero da Alhaji Nasiru Ado Bayero da wasu Sarakuna sun je wajen buda bakin da Muhammadu Buhari ya shirya a kasar Saudi.
Asali: Legit.ng