Buhari Ya Kammala Umrah, Ya Dawo Najeriya Bayan Shafe Kwanaki 8 a Kasar Saudiyya
- Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya dawo Najeriya bayan ziyarar Umrah na tsawon kwanaki takwas da ya yi a kasar Saudiyya mai tsarki
- Shugaban ya tarbi manyan jiga-jigan ‘yan Najeriya a Saudiyya a lokacin da ya hada taron buda baki na azumin Ramadana a ziyarar
- Ba wnanan ne karon farko da shugaban kasa Muhammadu Buhari ke zuwa Saudiyya domin ziyarar ibada ba
FCT, Abuja - Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya sauka a Abuja bayan shafe kwanaki takwas a tafiyarsa ta kasar Saudiyya ibadan Umrah, TheCable ta ruwaito.
Buhari ya baro kasar Saudiyya ne daga filin jirgin saman kasa da kasa na Sarki Abdulaziz da ke birnin Jeddah a ranar Laraba 19 Afirilu, 2023.
A cewar rahoton kamfanin dillacin labarai na Najeriya, gwamnatin Saudiyya, sarakunan gargajiya da malaman addini daga Najeriya da manyan jami’an jakadancin Najeriya a Saudiyya ne suka yiwa Buhari bankwana a Jeddah.
Buhari ya yi Umrah a ranar Alhamis din da ta gabata
A ranar Alhamis din da ta gabata, Buhari ya yi Umrah a Saudiyya zagaye da jami’an tsaro a lokacin da isa masallacin Makkah mai alfarma daga birnin Madina.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Hakazalika, Buhari ya kai ziyara wasu wuraren tarihi masu daraja a Madina a ranar Talata da Laraba kafin gangarawarsa zuwa Makka don ibadar Umrah, rahoton The Nation.
A bangare guda, a can birnin Makkah, Buhari ya karbi bakuncin manyan jiga-jigan Najeriya da suka hadu a can don yin buda bakin azumin Ramadana.
Musulami daga bangarori daban-daban na duniya na zuwa ziyarar aikin Hajji ko Umrah a kasar Saudiyya a lokuta daban-daba.
Duk da wannan, ba karon nan ne na farko da shugaban kasa Muhammadu Buhari yake kai ziyara kasa mai tsarki ba.
Ba lallai a yi sallar Idi ranar Juma’a ba, inji masana
A wani labarin kuma, rahoto ya bayyana cewa, ba lallai a yi sallar azumin Ramadana a ranar Juma’a mai zuwa ba duba da yanayi da kuma yadda watan Ramadana ya zo bana.
Wannan na zuwa ne daga wani hasashe da binciken da masana suka yi a daukar Larabawa, inda suka bayyana abin da suka hango na yanayin ganin watan Shawwal.
A cewarsu, a yankin Larabawa ba a za a ga wata ba a ranar Alhamis, don haka zai iya yiwuwa a tashi da azumi a ranar Juma’a.
Asali: Legit.ng