Innalillahi: Rai Ya Salwanta Yayin Da Mutane Dama Suka Jikkata a Wani Mummunan Hadarin Mota

Innalillahi: Rai Ya Salwanta Yayin Da Mutane Dama Suka Jikkata a Wani Mummunan Hadarin Mota

  • Wani mummunan haɗarin mota a jihar Legas ya janyo asarar ran mutum ɗaya yayin da wasu da dama suka jikkata
  • Wasu motoci guda biyu ne dai suka yi taho mu gama a mummunan haɗarin motan da ya auku a safiyar yau Laraba
  • Jami'an hukumar kula da harkokin sufuri ta jihar tuni suka isa wajen domin bayar da agajin gaggawa

Jihar Legas - Hukumar kula da harkokin sufuri ta jihar Legas (LASTMA) ta bayyana cewa wani mummunan haɗarin mota ya auku a ranar Laraba a Ifako, a yankin Ogudu na jihar.

Hukumar ta bayyana cewa motar BRT ta bas da wata motar haya ta bas suka ti taho mu gama a wani haɗari da ya auku da safiyar yau Laraba, cewar rahoton The Cable

Mummunan hadarin mota ya auku a jihar Legas
Motar BRT ta kife a mummunan hadarin Hoto: Thecable.com
Asali: UGC

A wani bidiyon da aka sanya a shafin LASTMA na Twitter, motar hayar bas ɗin wacce aka fi sani da 'Danfo' ta yi tungura gutsi bayan ta haɗe da motar BRT ɗin.

Kara karanta wannan

INEC Ta Kawo Karshen Kace-Nace, Ta Aika Sako Ga IGP Kan Kwamishinan Zaben Adamawa

Waɗanda suka tsira daga haɗarin an nuna su suna zaune a gefen inda mutane ke wucewa yayin da jami'an hukumar ta LASTMA, suke ƙoƙarin saita cunkoson ababen hawa, cewar rahoton Vanguard

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Hukumar ta fitar da wata sanarwa inda ta tabbatar da aukuwar haɗarin. Sanarwar na cewa:

"Haɗari ya auku a Ifako gabanin gadar Obudu tsakanin motar bas ta BRT da wata motar bas ta haya. An samu asarar ran mutum ɗaya, yayin da dama suka samu raunika."

LASTMA ta bayyana cewa ta tuntuɓi hukumar bayar da agajin gaggawa ta jihar (LASEMA) da hukumar kula da lafiyar gaggawa ta jihar (LASAMBUS) domin kawo ɗauki.

Hukumar ta kuma ƙara da cewa, jami'an ta sun iso inda haɗarin ya auku domin aiwatar da abinda ya dace.

Munanan Haduran Mota Sun Janyo Asarar Rayuka a Jihar Bauchi

Kara karanta wannan

Shin An Biya Kuɗin Fansa? Ɗalibai Mata Na Jami'ar Tarayya Gusau Sun Kubuta Daga Hannun Yan Bindiga

A wani labarin na daban kuma, wasu munanan haɗuran mota a jihar Bauchi sun janyo asarar rayukan bayin Allah da dama, yayin da wasu mutanen da dama suka rigamu gidan gaskiya.

Munanan haɗuran motan waɗanda suka auku a wurare daban-daban na jihar, sun janyo asarar rayukan mutum 9.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng