Tashin Hankali Yayin da Aka Sace Direban Mataimakin Gwamnan Jihar Nasarawa

Tashin Hankali Yayin da Aka Sace Direban Mataimakin Gwamnan Jihar Nasarawa

  • Rahoton da muke samu daga jihar Nasarawa na bayyana yadda aka sace direban mataimakin gwamnan jihar
  • An sace shi na a daren jiya a lokacin da ya kai ziyara gidan wani abokinsa, kamar yadda rahoto ya bayyana
  • Ya zuwa yanzu, 'yan sanda sun tabbatar da lamarin, suna ci gaba da bincike don gano yadda za a ceto shi

Jihar Nasarawa - Wasu ‘yan bindiga sun yi awon gaba da Daniel Ogoshi, direban mataimakin gwamman jihar Nasarawa, Dr Emmanuel Akabe.

The Nation ta ruwaito cewa, an sace Ogoshi ne a gidan wani abokinsa da misalin karfe 9:30 na dare a yankin Ombi 2 kusa da kwalejin noma da ke hanyar Kwandere a Lafiya, inda suka bar wayarsa da motarsa a wurin da suka sace shi.

Wani aboki na kusa dangi ya shaidawa ‘yan sanda abin da ya faru, inda suka yi gaggawar zuwa wurin da lamarin ya faru sai suka tarar an riga an tafi dashi.

Kara karanta wannan

Ba da Mace Nayi Takara ba – Fintiri ya Fadi Asalin Abokan Gwabzawarsa Bayan Ya Zarce

An sace direban mataimakin gwamna a Nasarawa
Jihar Nasarawa da ke Arewacin Najeriya | Hoto: channeltsv.com
Asali: UGC

An tabbatar da sace direban mataimakin gwamna

Hadimin mataimakin gwamnan, Emmaneul Eyima ya tabbatar da faruwar lamari, ya kuma kara da cewa, bai da wasu cikakkun bayanai game da abin da ya faru.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Nasarawa, DSP Ramhan Nansel ya tabbatar da faruwar lamarin ya kuma ce jami’ai na kan aiki a lamarin, Vanguard ta ruwaito.

Sai dai, ya ce ba zai yi karin bayani a kai ba har sai ya samu cikakkun bayanai da ya kamata ya sani game da farmakin tsagerun.

Ana yawan samun munanan hare-hare a Arewacin Najeriya, musamman a irin wadannan lokuta masu tada hankali.

Dalibai sun tsere daga hannun tsagerun 'yan bindiga

A wani labarin da muka ruwaito a baya, kunji yadda wasu tsagerun ‘yan bindiga suka sace ‘yan mata dalibai a jihar Kaduna, inda suka tsere cikin wani kungurmin daji da ke tsakanin Kaduna da jihar Neja.

Kara karanta wannan

Kaico: Sojoji suntakarkare, sun bindige dan sanda da ke bakin aiki a jihar Arewa

An ruwaito cewa, daliban sun yi nasarar tserewa daga hannun ‘yan ta’addan a cikin makon nan, inda gwamnati ta tabbatar dauko su daga inda suka fake.

Ya zuwa yanzu, ana ci gaba da basu kulawar asibiti kafin daga bisani a mika su ga iyayensu a yankin Kachia da ke Kudancin Kaduna.

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.