COVID-19: Gwamnatin Tarayya ta Raba N45bn, Jihohi 7 Ba Su Samu Sisin Kobo ba

COVID-19: Gwamnatin Tarayya ta Raba N45bn, Jihohi 7 Ba Su Samu Sisin Kobo ba

  • Gwamnatin tarayya ta fitar da N45bn, ta rabawa wasu a cikin jihohi a karkashin tsarin NG-Cares
  • Gwamnonin jihohi Ebonyi, Kogi, Taraba, Enugu, Ogun da Imo ba su samu komai a kason kudin ba
  • Ana sa ran ayi amfani da kudin a jihohin kasar wajen rage talaucin da annobar COVID-19 ta jawo

Abuja - Jihohi bakwai ba su amfana da tsarin NG-Cares da gwamnatin Muhammadu Buhari ta fito da shi a dalilin annobar cutar COVID-19 ba.

The Nation ta ce an kawo NG-Cares ne domin rage radadin COVID-19 domin farfado da tattalin arzikin kasar nan da ya noke a karshen 2020.

A dalilin haka gwamnatin tarayya ta raba gudumuwar Naira biliyan 45.3 ga wasu gwamnoni, amma akwai jihohin da ba su amfana da kudin ba.

Rahoton ya ce Benuwai, Taraba, Kogi, Ebonyi, Enugu, Ogun da Imo ba su iya samun tallafin ba saboda ba su biya abin da suka fara karba ba.

Kara karanta wannan

Kaico: Bashi ya yi mata katutu, ta siyar da jaririyarta mai watanni 18 kacal a wata jiha

Jihar Imo tayi rashi biyu

Tun farko gwamnatin Imo ba ta samu ko kobo daga cikin tallafin ba, saboda haka da aka tashi rabon zagaye na biyu na NG-Gares, ba ta cikin lissafi.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Karamin Ministan kasafi, tsare-tsaren tattalli da arziki, Clem Agba, ya bada sanarwar cewa jihohi 29 da kuma Abuja suka samu kaso na biyu na kudin.

FEC Abuja
Taron FEC a Abuja Hoto: @BuhariSallauOnline
Asali: Facebook

This Day ta rahoto Jami’in sadarwa da yada labaran NG-CARES, Suleiman Odapu yana cewa tsarinsu ya yi nasarar cin ma manufofin da aka kawo.

A cewar Suleiman Odapu, tun ranar Alhamis da ta wuce, gwamnati ta maidawa jihohi 29 abin da ya kai N45bn ganin sun dawo da abin da suka karba.

Jihohi uku da suka yi kokari wajen maido kudin su ne: Zamfara mai N5,273,150,000.00, Bauchi da N4,232,200,000.00 da Ondo, N3,838,233,411.00.

Kara karanta wannan

IRev Ta Tona Magudi da Aka Shirya Domin APC da Tinubu Su Ci Zaben Jihar Ribas

Clement Agba ya yi rawar gani

Ana sa ran hakan zai taimaka sosai wajen magance matsalar talauci a jihohin kamar yadda aka tsara.

A jawabin da ya yi a jiya, Odapu ya yabi Agba saboda rawar da ya taka wajen hada-kan gwamnatocin tarayya da jihohi da bankin Duniya a kan tsarin.

Aishatu Dahiru Binani ta wanke kan ta

A wani jawabi da ta fitar da aka bada sanarwar Ahmadu Umaru Fintiri ya ci zabe, Aishatu Dahiru Binani ta wanke kan ta daga zargin bada cin hanci.

‘Yar takarar APC a zaben Gwamnan Adamawa, Sanata Binani ta ce ba za ta taba daukar siyasa a mutu ko ayi rai ba, ta ce ba yau ta faara shiga zabe ba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng