Mata Ta Yi Karar 'Mijinta' A Kotun Shari'ar Musulunci A Kaduna Kan Ƙin Kai Ta Saudiyya
- Wata mata mai suna Karima Nuhu yar shekara 45 ta garzaya kotun shari'ar musulunci da ke unguwar Rigasa a Kaduna ta yi karar 'mijinta' Musa Falalu
- Karimatu ta shaida wa kotu cewa Falalu ya mata alkawarin za su tafi Saudiyya tare hakan yasa ta ciyo bashi amma bayan ya samu abin da ya ke ya sake ta sai dai babu shaida
- Falalu ya musanta wannan zargin ya kuma shaida wa kotu cewa ya saki Karima, alkalin kotu ya ce ba zai iya hukunci kan lamarin ba tunda ta ce babu wanda ya shaida faruwar abin
Rigasa, Kaduna - Wata mata yar shekara 45, Karima Nuhu, a ranar Talata ta maka mijinta, Musa Falalu, a kotun shari'ar musulunci da ke zamanta a Rigasa, kan cewa bai kai ta Saudiyya ba.
Bayan Shafe Shekaru a Amurka, Matashiya Ta Dawo Najeriya Ta Ga Lalataccen Gidan Da Dan Uwanta Ya Gina Mata, Ta Sharbi Kuka
Wacce ta yi karar, mazauniyar unguwar Rigasa da ke Kaduna, ta fada wa kotun cewa shekarunta hudu tana auren Falalu, amma wata biyu kacal ya yi yana ba ta abinci, Daily Trust ta rahoto.
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
Ta ce:
"Ya fada min ya rasa aikinsa na tuki amma ya samu wani aikin a kasar Saudiyya, ya bukaci in yi hakuri yayin da ya yi alkawarin zamu tafi tare.
"Kawo yanzu, ni ne ke ciyar da kaina. Har bashin kudi na ciyo masa saboda ya samu ya biya kudin tafiyar, amma bayan ya samu abin da ya ke so, sai ya sake ni."
Ba ni da wani shaida sai Allah (SWT) - Karima
Ta fada wa kotu cewa ba ta da wani shaida kan wannan zargin sai dai Allah (SWT) wanda zai musu hisabi a ranar gobe kiyama.
Wanda aka yi karar, Falalu, ya musanta zargin da ta yi a kansa.
Ya fada wa kotun cewa shi ya riga ya saki wacce ta shigar da karar.
Hukuncin da kotu ta yanke
Alkalin kotun, Mallam Anass Khalifa, wanda ya tabbatar da cewa mijin ya saki matarsa, ya ce kotun ba za ta iya sauraron zargin da matar ta yi ba domin babu shaida.
Mata Ta Yi Karar Mijinta Tana Son A Raba Aurensu Don Rashin Haihuwa
A wani rahoton kun ji cewa kotun kwastamare da ke zamanta a birnin tarayya Abuja ta raba aure tsakanin wata mata mai suna Blosom Ameh da mijinta Simon, saboda rashin haihuwa.
Bangarori biyun sun shaida wa alkalin kotun cewa ba su son cigaba da zaman aure don haka Alkalin kotun, Doocivir Yawe, ya datse igiyar aurensu na shekara 10.
Asali: Legit.ng