Wani Dan Shekara 37 Ya Wawushe Naira Miliyan 21 Daga Asusun Coci A Legas

Wani Dan Shekara 37 Ya Wawushe Naira Miliyan 21 Daga Asusun Coci A Legas

  • Yan sanda sun yi karar wani Nwafor Onyebuchi dan shekara 37 a kotu kan zarginsa da sace N21 daga coci
  • A yayin gabatar da karar, yan sandan sun yi ikirarin cewa Onyebuchi ya aikata laifin ne a Disamban 2022 a cocin Katolika na St. Patrick, Alaba, Ojo a Legas
  • Wanda ake zargin ya musanta aikata laifin kuma kotu ta bada belinsa kan Naira miliyan 1 sannan ta saka ranar fara shari'a

Legas - Rundunar yan sandan Legas ta gurfanar da wani mutum dan shekara 37 mai suna Nwafor Onyebuchi a Kotun Majistare na Legas mai zamansa a Badagry kan satar N21m daga cocin katolika.

Yan sandan sun gurfanar da Onyebuchi ne kan laifuka uku masu alaka da hadin baki, sata da kuma tada zaune tsaye, The Punch ta rahoto.

Kara karanta wannan

Kaico: Bashi ya yi mata katutu, ta siyar da jaririyarta mai watanni 18 kacal a wata jiha

Kotun Majistare Legas
An gurfanar da wani dan shekara 37 kan satar N21m na coci a Legas. Hoto: The Punch
Asali: Facebook

Dan sanda mai gabatar da kara, Sufeta Ayodele Adeosun, ya shaidawa kotu cewa wanda aka yi karar ya aikata laifin ne a ranar 21 ga watan Disamban 2022, a cocin Katolika na Saint Patrick da ke Alaba a Ojo, jihar Legas.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Ya ce wanda aka yi karar ya sace kudin da aka ware ne don ayyukan cigaban coci.

Adeosun ya bayyana cewa wanda aka yi karar ya yi amfani da kudin don wasu bukatun kansa.

Mai gabatar da karar ya kuma shaida wa kotu cewa wanda ake tuhumar ya aikata abin da ka iya tada rikici a cocin saboda sace kudin, Vanguard ta rahoto.

A cewar mai shigar da karar, laifin ya saba da tanade-tanaden sashi na 287, 168 da 307 na Dokar Masu Laifi na Jihar Legas, 2015.

Kara karanta wannan

Daga karshe: Bayan dogon kai ruwa rana, Ado Doguwa ya lallasa dan tsagin Kwankwaso

Amma, wanda ake tuhumar ya musanta aikata laifin da aka zarginsa.

An bada belin wanda ake zargi

Sannan, Alkalin kotun, T.A. Popoola, ya bada belin wanda ake zargin kan kudi N1m tare da mutane biyu da za a bada shi hannunsu belin.

Popoola ya umurci daya cikin wadanda za su karbi belin wanda ake tuhumar ya kasance danginsa, sannan dukkansu biyu su gabatar da hujjar biyan haraji ga gwamnatin Legas na shekara uku.

Ya dage cigaba da shari'ar zuwa ranar 5 ga watan Yuni don fara saurare.

Yan sanda sun cafke wata mata kan satar kudin coci

A wani rahoton, yan sanda sun kama wata matar aure da ke goyon jinjiri dan wata guda kan satar kudi mallakar coci.

An kama Judith Nanangwe ne yar shekaru 24 kuma aka gurfanar da ita a kotun majistare na Valerian Tuhimbise da ke Kampala a Uganda.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164