Satar sadakar coci: 'Yan sanda sun kama mata mai shekaru 24

Satar sadakar coci: 'Yan sanda sun kama mata mai shekaru 24

- Judith Nanangwe, matar aure ce da ke da goyon jariri mai wata daya a duniya

- 'Yan sanda sun damke ta ne bayan da aka kama ta dumu-dumu da laifin sata a coci

- An yanke mata hukuncin biyan Shs250,000 bayan ta amsa laifinta da sungume jakar da ke kunshe da sadakar da masu bauta suka bada a coci

Judith Nanangwe, matar aure ce da ke da goyon jariri mai wata daya a duniya. 'Yan sanda sun damke ta ne bayan da aka kama ta dumu-dumu da laifin sata a coci.

Matar auren mai shekaru 24 na zama ne a titin Kob da ke Seeta a yankin Mukuno. Ta kuma gurfana ne a gaban wata kotun majistare da ke Valerian Tuhimbise a garin Kampala da ke Uganda, kamar yadda within Nigeria ta ruwaito.

An yanke mata hukuncin biyan Shs250,000 bayan ta amsa laifinta da sungume jakar da ke kunshe da sadakar da masu bauta suka bada a coci. Jakar na dauke ne da Shs643,000 kuma ta zama mallakin cocin.

Satar sadakar coci: 'Yan sanda sun kama mata mai shekaru 24
Satar sadakar coci: 'Yan sanda sun kama mata mai shekaru 24
Asali: UGC

DUBA WANNAN: Banda bautar Allah, jima'i shine abinda yafi komai muhimmanci a rayuwa - Jaruma Juliet Njemanze

Mai shari'a Tuhimbise ya ce an yanke mata hukuncin biyan Shs250,000 ne ganin halin da jaririnta yake ciki. Amma kuma cocin ta bukaci a garkame Nanangwe a gidan gyran hali tare da daukar watanni ana bata shawarwari.

Amma kuma Nanangwe da kanta ta ce tayi dana-sanin abinda tayi don taje cocin ne don ta sauya hali. Don hakan akwai bukatar ta samu shawarwari.

Amma kuma idan ta gaza biyan Shs250,000, dole za ta sa ta zauna a gidan yari na watanni biyar.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng