‘Zama Uwa Babu Sauki’: Wata Uwa Ta Sha Wahala, Ta Ce Zama Uwa Ba Aiki Ne Mai Sauki Ba

‘Zama Uwa Babu Sauki’: Wata Uwa Ta Sha Wahala, Ta Ce Zama Uwa Ba Aiki Ne Mai Sauki Ba

  • Wata uwa ta bayyana cewa, ba aiki ne mai sauki ba kasancewarta uwa sabanin abin da ake fada a kafafen sada zumunta
  • Matar ta yada wani bidiyo a kafar sada zumunta, inda ta nuna yadda take goyon ‘ya’yanta tagwaye a lokaci daya
  • Mutane da yawa sun yi ta cece-kuce kan yadda matar ta shiga yanayi, inda wasu ke cewa su suna fatan Allah ya basu ‘yan uku

An yi ta cece-kuce a kafar sada zumunta a lokacin da wata mata ta yada bidiyon cewa, aikin kasancewa uwa ba karamin aiki ne mai sauki ba.

A cikin bidiyon da ta yada a TikTok, matar mai suna @trishaitua a kafar ta ce, mata su daina yaudaruwa da cewa aikin reno na uwa abu ne mai sauki.

A cewarta, yanzu haka tana da jarirai guda biyu tagwaye, kamar yadda aka ga tana goye dasu a cikin bidiyon da ta yada.

Kara karanta wannan

“Soyayya Bata Tsufa”: Tsohuwa Mai Dogara Sanda Ta Amarce Da Sahibinta, Bidiyon Ya Yadu

Mata tace renon yara ba sauki
Yadda mata ta goyi jarirai biyu a baya | Hoto: TikTok/trishaitua
Asali: UGC

Goyon jarirai biyu a lokaci daya

Abin da ya ja hankalin jama’a, an ga lokacin da matar ke goye da ‘ya’yanta tagwaye guda biyu a baya kana tana aikin madafa.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A bayyane yake cewa tagwayen a bata wahala, wanda alamu suka nuna shine dalilin da yasa ta goye su lokaci daya.

Wannan yasa ta ayyana cewa, zama uwa da reno ba aiki ne mai sauki ba, a daina yada saukinsa a kafar sada zumunta ‘yan mata na yaudaruwa.

Ayyanawarta ya sanya mutane da yawa a kafar TikTok yin martani mai daukar hankali tare da bayyana ra’ayoyinsu.

Wasu sun ce ta yi gaskiya, wasu kuwa suka ce sam bata gane bane, wasu kuma suka ce suna bukatar Allah ya basu ‘yan uku.

Kalli bidiyon:

Martanin jama’a

@Official_kktwins:

"Har yanzu ina son ‘yan uku.”

@giftpual295:

"Ya Allah, ina rokon wannan albarkar da sunan Annabi Isa, Amen.”

Kara karanta wannan

“Ta Gaji Da Auren Tun Ba a Kai Koina ba” Bidiyon Amarya Tana Kicin-Kicin Da Rai Yayin da Take Jerawa Da Angonta Ya Yadu

@ensamabbsbeautyplace:

"Babu sauki fa, na taba shiga irin yanayin nan. Allah ya ja ran tagwaye.”

@Wisy J. Johnson:

"Kai, Allah ya kare wadannan yaran...kin ba ni sha’awar naje na yi aure kawai.”

@priscillanartey88:

"Allah ya ba ki babban kyauta.”

Duk dai dadin haihuwa, wata mata kuwa daukar jaririyarta ta yi mai watanni 18 kacal ka siyar da ita saboda cin bashin banki da ta yi.

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.