Fintiri Ga ’Yan Adamawa: Ina Neman Afuwarku Game da Ciwon Zuciyan da Aka Sanya Muku

Fintiri Ga ’Yan Adamawa: Ina Neman Afuwarku Game da Ciwon Zuciyan da Aka Sanya Muku

  • Gwamnan jihar Adamawa ya bayyana kalaman godiya da jin dadi bayan da aka sake zabansa a karo na biyu
  • Ya kuma ba masoyansa hakuri bisa karya musu zuciya da aka yi a zaben cike gurbin da aka gudanar a ranar 15 ga watan Afrilu
  • Daga karshe, ya mika sako ga abokan hamayyarsa na jam’iyyu daban-daban na jihar a zaben na bana

Jihar Adamawa - Zababben gwamnan jihar Adamawa, Ahmadu Fintiri ya ba magoya bayansa hakuri bisa ciwon kai da aka sanya musu na kakaba musu gudanar zaben cike gurbi a jihar.

Jaridar Punch ta ruwaito cewa, hukumar zabe mai zaman kanta (INEC) ta ayyana Fintiri a matsayin wanda ya lashe zaben 2023 a jihar Adamawa a ranar Talata 18 Afirilu, 2023.

Baturen zabe a jihar, Muhammad Melee, ya bayyana cewa, Fintiri na PDP ya samu kuri’u 430,861 yayin da Aisha Binani na APC ta samu kuri’u 398,788 a zaben na bana.

Kara karanta wannan

Ba da Mace Nayi Takara ba – Fintiri ya Fadi Asalin Abokan Gwabzawarsa Bayan Ya Zarce

Fintiri ya yi bayani bayan lashe zabe
Jihar Adamawa da ke Arewa maso Gabas | Hoto: channelstv.com
Asali: UGC

Nasarar Fintiri na zuwa ne kwanaki hudu biyu kenan da kwamishinan zaben jihar, Hudu Ari ya yi kuskuren sanar da Binani a matsayin wacce ta lashe zaben jihar.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sanarwar tasa ta jawo INEC ta gaggauta dakatar da tattara sakamakon zaben, wanda a yau Talata 18 Afirilu, 2023 aka ci gaba da tattara shi har aka kammala sanar da wanda ya lashe.

Kalaman ba da hakuri da karbar nasara daga Fintiri

A jawabansa na karbar nasara da daren Talata, Fintiri ya ba masoyansa a Adamawa hakuri bisa sanya musu ciwon kai da firgici da ciwon zuciya a lokacin da aka dage tattara sakamakon zaben jihar.

Hakazalika, ya ce zai ci gaba da yiwa ‘yan jiharsa ayyukan da ya dauko na ciyar da jihar Adamawa gaba, Within Nigeria ta ruwaito.

Yayin da yake taya abokan hamayyarsa murnar yin kokari a zaben gwamnan, ya yi Allah wadai da yadda Hudu Ari ya ayyana Binani a matsayin wacce ta lashe zabe.

Kara karanta wannan

Daga karshe: INEC ta kammala zaben Adamawa, gwamna Fintiri ya koma kujerarsa

Muhammad Abdulrazak, wani mai sharhi kan harkar siyasa a Adamawa ya ce, nasarar Fintiri ba abin mamaki bane, domin an so murde zaben a baya.

A cewarsa:

"Da jin sanar da Binani kasan akwai kauje cikin nadi, don haka wannan daidai ne, kuma mun gode da gwamna ya yi mana jawabi kan matsayarsa."

An sanar da sakamakon zaben jihar Adamawa

A wani labarin, kunji yadda hukumar zabe ta INEC ta bayyana sakamakon zaben gwamnan jihar Adamawa a yau Talata 18 Afirilu, 2023.

Hakan na zuwa ne bayan kammala zaben cike gurbin da aka gudanar a ranar 15 ga watan Afrilun bana.

An samu tsaiko a Adamawa bayan da aka ayyana Binani a matsayin wacce ta lashe zaben kafin tattara sakamakon zabe.

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.