Sojoji Sun Sheke Jami’in Dan Sanda Saboda Kama Abokin Aikinsu da Tabar Wiwi
- Rahoton da muke samu daga jihar Borno ya bayyana yadda wani dan sanda ya mutu a hannun jami’an sojoji a jihar
- Wannan ya faru ne a shingen binciken ababen hawa a Benisheikh, inda ‘yan sanda suka tare motar wani soja dauke da tabar wiwi
- Ana yawan samun matsala tsakanin sojojin Najeriya da ‘yan sanda kan lamuran da basu taka kara sun karya ba
Jihar Borno - Wasu sojoji sun bindige wani sajan din dan sanda mai suna Ahmed Ali a garin Benisheikh da ke jihar Borno bayan da ya kama wani soja a cikin wata mota dauke da tabar wiwi.
Mazauna da kuma majiyar sun shaidawa Daily Trust cewa, lamarin ya faru ne a shingen bincike da ke mashigar garin da misalin karfe 10 na safe a ranar Litinin.
Majiyar tsaro ta ce, sojan ya zo ne a cikin wata mota mai launin toka da lambar FKJ 761 AR, inda ya buge jami’in tsaron da ke shingen tare da kin tsayawa a wurin.
Yadda lamarin ya faru daga majiya
A cewar majiyar:
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
“Kin tsayawa da ya yi yasa ‘yan sanda suka harbi tayarsa, wanda hakan yasa ya tsaya; amma a kokarin kai motar ta ofishin ‘yan sanda na Benisheikh, sojoji suka harbe Sgt Ali.
“Sojan da ke dauke da tabar wiwi mai suna Sgt U.Joseph tare da abokan aikinsa, sun yi kokarin hana ‘yan sanda tafiya da motar, wanda hakan ne ya kai ga harbi har aka samu Sgt Ali da ke kokarin yin baya da motar.”
An tattaro cewa, a halin yanzu, sojan da ake zargi da harbin na can a tsare a hannun jami’an soja, ita kuwa motar an ajiye ta a ofishin ‘yan sanda da ke Benisheikh.
Kuskure ne, ana ci gaba da bincike
Wata majiya daga gidan soja ta bayyana cewa, an yi harbin ne cikin kusa, inda yace wani soja mau suna Ibrahim Waberi ne ya yi harbin don hana tafiya da motar, Tori ta tattaro.
A cewar majiyar:
“Harbinsa ya yi kuskuren samun mamacin ne amma wanda ake zargin yana tsare ana ci gaba da bincike.”
An yi kokarin jin ta bakin kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Borno, ASP Sani Kamilu Shatambaya, amma bai yiwu ba, domin yana kan hutu, kuma ba asamu jin ta bakin mataimakinsa ba.
An taba samun wnai sojan da ya sheke dan sanda saboda rikicin da ya barke a tsakaninsu saboda budurwa.
Asali: Legit.ng