Soja ya kashe dan sanda a filin daga saboda budurwa
Wani soja mai matsayin Kofur ya kashe wani dan sanda da bindigar harbo jirgin sama mai kirar AAG, bayan fada a kan budurwa da ya shiga tsakaninsu. Lamarin ya faru ne a yankin Makara da ke karamar hukumar Gwoza ta jihar Borno.
PRNigeria ta gano cewa, kofur din ya kashe dan sandan mai matsayin sajan mai suna Rowland Tafida ne ba tare da hukunci daga kotu ba. An tura dan sandan ne karkashin runduna ta musamman da aka tura Gwoza don yaki da ta’addanci.
An gano cewa, Rowland mahaifin yara biyun na shirin barin Borno ne zuwa ranar Asabar mai zuwa kafin wannan mummunar kisan gillar ta biyo baya.
Ganau ba jiyau ba, wanda ya zanta da jaridar PRNigerian ya kwatanta kisan dan sandan Rowland da abu mafi muni da ya taba gani.
Ya ce an fara rigima tsakanin sojan da dan sandan ne a kan budurwa, wacce wasu jami’ai suka shiga cikin don sasantasu.
DUBA WANNAN: Yanzu-yanzu: Ganduje, 'yan majalisa da sarakuna sun kai wa Buhari ziyara (Hotuna)
Bayan kammala sasancin ne sojan ya umarci matukin motar yakin sansanin da ya juya kan motar. Juyawarsa ke da wuya kuwa ya bude wa sansanin ‘yan sandan wuta wanda yayi sanadiyyar mutuwar dan sandan.
“Wannan bude wutar da yayi wa dan sandan ya kawo lalacewar cinyar hagu ta dan sandan. Ya kwanta face-face cikin jini amma ba a mika shi asibiti da wuri ba. Hakan kuwa yayi sanadin mutuwar shi a take,” cewar majiyar.
Wata mata da ta ga abinda ya faru, ta ce tuni ‘yan sanda suka fara zanga-zanga a sansanin sakamakon kisan gillar da aka yi wa daya daga cikinsu. Fitowar wani babban soja mai matsayin manjo ne yasa suka lafa sannan zaman lafiya ya dawo sansanin.
Amma kuma, duk kokarin PRNigeria na son jin ta bakin kakakin rundunar sojin Najeriya da ‘yan sanda ya tashi a tutar babu.
Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng