“Kana Jin Dadinka”: Matashi Ya Baje Koli Kyawawan Matansa 2, Mutane Sun Yi Masa Tambayoyi

“Kana Jin Dadinka”: Matashi Ya Baje Koli Kyawawan Matansa 2, Mutane Sun Yi Masa Tambayoyi

  • Wani matashi dan Najeriya ya nunawa duniya kyawawan matansa biyu cike da alfahari yayin da suka yi hotuna iri-iri
  • Matashin ya fada wa mutane cewa matan nasa na zaman amana da juna yayin da ya kwatanta alakarsu da ta tagwaye
  • Mutane da dama a sashin sharhi sun so sanin yadda matan ke samun kulawa ba tare da kishi ba

Wani matashi dan Najeriya, @jagunmoluibile, wanda ke da matan aure biyu, ya wallafa wani bidiyo da ke nuno dukkansu sanye da tufafi iri daya.

Mutane da dama sun cika da mamakin yadda iyalin suka hadu shar da su. Don nuna cewa akwai kyakyawar alaka da fahimtar juna tsakanin kyawawan matan nasa biyu, ya kira su da tagwaye.

Miji tare da kyawawan matansa biyu
“Kana Jin Dadinka”: Matashi Ya Baje Koli Kyawawan Matansa 2, Mutane Sun Yi Masa Tambayoyi Hoto: @jagunmoluibile
Asali: TikTok

Matashi na farin ciki da matansa biyu

A cikin wani bidiyon, mutumin ya nuna matayen nasa da yara sannan ya yi masu lakabi da hannun jarinsa. A daya daga cikin hotunansu, duk sun sanya wando da riga da kuma takalmi iri guda.

Kara karanta wannan

Bidiyon Yadda Malamin Kwaleji Ya Dauki Jinjirin Dalibarsa Cike Da Sakin Fuska Ya Yadu, Jama’a Sun Jinjina Masa

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Bidiyon nasu wanda ya yadu ya haddasa cece-kuce yayin da mutane suka tambaye shi kan yadda aka yi aurensu ke tafiya daidai.

Kalli bidiyon a kasa:

Bidiyon ya tattara martani fiye da 400 da kuma'likes' fiye da 23,000.

Jama'a sun yi martani

Mimi ta ce:

"An yi amfani da aure wajen mayar da ku tagwaye."

user9606204733394 ya ce:

"Nawa shine wa ke zama a gaba."

Ölûwåtõsïn ta ce:

"Ba zai taba zama ni ba yi hakuri."

omodano ya ce:

"Kana jin dadi. Allah ya albarkaci gidanku."

Da_girl_Ruby ta ce:

"Wa ke zama a kujerar gaba dan Allah??"

Slim_funnybaeta yi ba'a:

"Uwargida ke tuki amarya na zama a gefe a kujerar gaba, mijin na zaune hankali kwance a baya."

Lady_dbabe ta ce:

"Kuna kokari gaskiya....amma ba zai taba zama ni ba.....Nawa nake so ba namu ba."

Kara karanta wannan

“Na Zata Zan Yi Aure Ina Da Shekaru 22”: Dirarriyar Budurwa Ta Bayyana Yadda Rayuwarta Ta Sauya Bayan Shekaru a Bidiyo

MEMEKOOL ya ce:

"Ba mu yi aure ba kai ka yi gaggawan daukar biyu ka ajiye a gida...."

Matashi ya yi wuff da aminyarsa da suka shafe shekaru 10 suna soyayya

A wani labarin, wasu ma'aurata sun tsuma zukata da dama bayan amaryar ta ba da labarin yadda Allah ya hada ta da angonta tun suna kananan yara a makaranta, an haife su a rana daya kuma a gari guda.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng