Mawaki Rarara Ya Nemi Kotu Tayi Watsi Da Karar Da Ake Masa
- Sanannen mawaƙin siyasar nan Dauda Kahutu Rarara, ya nemi kotu ta yi fatali da tuhumar da ake masa a gaban ta
- Wani ɗan kasuwa ne dai ya maka Rarara a gaban kotun shari'ar musulunci kan ƙin biyan sa haƙƙin sa na kasuwancin da suka yi
- Mawaƙin ya musanta zargin ƙin biyan kuɗaɗen da ake masa wanda adadin yawan su ya kai N10m
Jihar Kano - Shahararren mawaƙin siyasar nan, Dauda Kahutu Rarara, ya buƙaci wata kotun shari'ar musulunci mai zama a jihar Kano, da ta yi fatali da ƙarar sa da aka shigar a gaban ta.
Jaridar Daily Trust ta kawo rahoto cewa ana tuhumar Rarara da ƙin biyan wani ɗan kasuwa mai suna Muhammad Ma'aji, kuɗaɗen sa da yawan su ya kai sama da N10m.
Tun da farkon fara shari'ar mawaƙin bai samu halartar sauraron ƙarar da ake masa ba, cewar rahoton Daylight reporters
A yayin zaman kotun da aka ci gaba a Rijiyar Zaki, wacce mai shari'a Halhalatul Khuza’i Zakariyya, ke jagoranta, lauyan da ke kare Rarara, G. A. Badawi, ya gaya wa kotun cewa ƙarar ba ta da tushe ballantana makama saboda haka yakamata ayi fatali da ita.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Ya ƙara da cewa sun mayar da martanin su a rubuce kan ƙorafin da kotun, amma masu shigar da ƙara sai suka ce sun ga martanin a ƙurarren lokaci yayin da kotun ke shirin fara zaman ta.
Mai shigar da ƙorafin, Muhammad Ma'aji, ya gayawa kotun cewa yana da dukkanin hujjojin sa a rubuce waɗanda za su tabbatar da zargin da yake cewa tun lokacin da suka fara harƙallar kasuwanci da Rarara a shekarar 2021, bai bashi ko sisi ba.
Mai shari'a Halhalatul Khuza’i Zakariyya ya umurci lauyoyi masu shigar da mayar da martanin su a rubuce ga lauyoyi masu kare wanda ake ƙara da kuma kotun.
Mai shari'a Zakariyya ya ɗage sauraron ƙarar har sai zuwa ranar 12 ga watan Mayun, 2023 domin cigaba da sauraron ɓangarorin biyu.
An Kama Yan Sanda Da Ke Ba Wa Rarara Tsaro
A wani rahoton na daban kuma, kun ji yadda aka cafke ƴan sandan da ke ba mawaƙin siyasar nan, Dauda Kahutu Rarara, kariya.
Rundunar ƴan sanda na tuhumar su da nuna rashin iya ƙwarewa a fannin aiki bayan sun harba bindiga sama a cikin bainar jama'a.
Asali: Legit.ng