Abubuwa Sun Tsaya Cak Yayin Da Ma'aikatan Filin Jirgin Sama Suka Shiga Yajin Aiki A Najeriya

Abubuwa Sun Tsaya Cak Yayin Da Ma'aikatan Filin Jirgin Sama Suka Shiga Yajin Aiki A Najeriya

  • Fasinjoji a filin jiragen saman Najeriya sun yi cirko-cirko bayan ma'aikatan filin jirgin sun shiga yajin aiki
  • Ma'aikatan dai sun tsunduma yajin aikin ne na gargaɗi na kwana biyu kan wasu buƙatun da suke so a cika mu su
  • Yajin aikin na zuwa ne bayan taron neman sulhu da ma'aikatan domin hana su shiga yajin aikin bai haifar da ɗa mai ido ba

Jihar Legas - An samu tsaiko a ɓangaren zirga-zirgar jiragen sama na Najeriya inda fasinjoji da dama suka yi cirko-cirko bayan ƙungiyoyin ma'aikatin filin jirgin sama sun shiga yajin aikin gargaɗi na kwana biyu.

Jaridar Punch ta rahoto cewa mambobin ƙungiyoyin sun rufe ƙofar shiga ɓangaren tashin jiragen cikin gida na filin jirgin sama na Murtala Muhammad da ke Legas, wanda hakan ya sanya fasinjoji da dama cirko-cirko.

Kara karanta wannan

Shugaba Buhari Ya Sanya Baki a Rikicin Sudan, Ya Aike Da Wani Muhimman Sako

Yajin aikin ma'aikatan jirgin sama ya sanya fasinjoji shiga garari
Fasinjoji sun yi cirko-cirko a filin jirgin sama na Murtala Muhammad, a dalilin yajin aikin ma'aikata Hoto: Vanguard.com
Asali: UGC

Hakan ya biyo bayan rashin samun mafita da aka yi a taron da hukumar Nigeria Civil Aviation Authority (NCAA) ta yi da ƙungiyoyin inda suka toge sai sun shiga yajin aikin.

Darekta Janar na hukumar NCAA, Capt. Musa Nuhu shine ya kira taron domin ba ƙungiyoyin baki sun janye yajin aikin gargaɗi na kwana biyu da suka shirya shiga, cewar rahoton Daily Trust

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Sakataren din-din-din na ministirin sufurin jiragen sama, Dr Emmanuel Meribole, ya samu halartar taron.

Sun bayyana buƙatun su

Ƙungiyoyin suna neman buƙatu da yawa daga ciki akwai, dakatar da shirin rushe hedikwatar NCAA a Legas da kuma da kiran a aiwatar da yarjejeniyar kula da jindadin ma'aikata da aka cimma da hukumar.

Jami'an tsaro da suka haɗa da ƴan sanda da sojoji suna a filin jirgin yayin da ƙungiyoyin suke rera waƙoƙin nuna haɗin kai.

Kara karanta wannan

Kano: Yan Sanda Sun Cafke Wasu Mutum 3 Bisa Tilasta Wani Almajiri Cin Bahaya Ana Azumi

NDLEA Ta Kama Mata Mai Juna Biyu Da Wani Gurgu Kan Safarar Miyagun Kwayoyi

A wani rahoton na daban kuma, kun ji yadda jami'an hukumar hana sha da fataucin miyagun ƙwayoyi (NDLEA), suka yi caraf da wata mata mai ɗauke da juna biyu da wani gurgu masu safarar miyagun ƙwayoyi.

Mutum biyun masu wannan baƙar sana'ar dai sun shiga hannun jami'an hukumar ne a jihar Edo.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng