Jam’iyyar APC Ta Fi Yawan Sanatoci a Majalisa Ta 10 da Za a Rantsar a Watan Yuni

Jam’iyyar APC Ta Fi Yawan Sanatoci a Majalisa Ta 10 da Za a Rantsar a Watan Yuni

  • Jam’iyyar APC ke da mafi yawan sanatoci a majalisar dattawa ta 10 da za a rantsar a watan Yunin wannan shekarar
  • An yi zaben cike gurbi, tuni sakamakon zaben ya fito, an ayyana wadanda suka yi nasara da kuma adadin kuri’unsu
  • A bangare guda, an samu tashin hankali bayan sanar da Aisha Dahiru Binani a matsayin sabuwar gwamna a jihar Adamawa

Najeriya - Jam’iyyar APC ce har yanzu mai rinjaye a majalisar dattawa ta kasa, inda ta kara samun yawan kujeru a zaben cike gurbin da aka kammala ranar Asabar.

Hukumar zabe ta INEC ta gudanar zabukan cike gurbi a mazabun sanata bakwai a jihohin Yobe, Kebbi, Sokoto, Zamfara da Filato.

Jam’iyyar APC ta yi nasarar lashe kujeru 55 bayan zaben 25 ga watan Faburairu, wanda a yanzu take da kujerun sanata 59 kenan a majalisar, rahoton The Nation.

Kara karanta wannan

Jerin Matan Arewa Da Suka Ciri Tuta A Siyasar Najeriya Da Maza Suka Yi Kaka-Gida

APC ta yi nasarar zama mafi rinjaye a majalisar dattawa
Majalisar dattawan Najeriya | Hoto: dailypost.ng
Asali: UGC

Majalisa ta 10 na da akalla sanatoci daga jam’iyyu 8

Akalla, jam’iyyun siyasa takwas ne ke da wakilai a majalisa ta 10 da za a rantsar nan ba da jimawa ba, wanda hakan ya zama tarihi a majalisar tare da jam’iyyu da yawa.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Babbar jam’iyyar dawa ta PDP na da kujeru 36, sai jam’iyyar Labour mai kujeru takwas da kuma NNPP ta su Kwankwaso mai kujeru biyu.

Jam’iyyar SDP na da kujeru biyu na sanata, sai kuma YPP da APGA da ke da sanata daya kowanne a majalisar ta 10, Daily Trust ta ruwaito.

A halin da ake ciki, an kammala zaben na cike gurbi, kuma tuni sakamakon zaben ya fito har an ayyana wadanda suka yi nasara.

Idan baku manta ba, a watan Yunin bana ne za a rantsar da majalisa ta 10 bayan karewar ta tara da ke shirin sallama nan ba da jimawa ba.

Kara karanta wannan

Zaben yau Asabar: Mata sun tona asirin APC a jihar Arewa, sun fadi yadda ake ba su kudi

Yadda rikici ya barke bayan sanar da zaben Adamawa

A wani labarin, kun ji yadda aka samu tsaiko a jihar Adamawa a lokacin da jami’in hukumar zabe ta INEC ya ayyana Aisha Binani a matsayin wacce ta lashe zaben gwamnan jihar.

Wannan na zuwa ne bayan yin zaben cike gurbi a ranar Asabar 15 ga watan Afrilu don karasa zaben da aka fara a ranar 18 ga watan Maris.

Ya zuwa yanzu, hukumar zabe mai zaman kanta ta nesanta kanta da sakamakon zaben da jami’in ya sanar tare da bayyana matakin gaba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.