INEC Ta Ce Abdulsamad Dasuki Ne Ya Lashe Zabe a Mazabar Tambuuwal/Kebbe a Majalisar Wakilai
- Rahoto daga jihar Sokoto ya ce, dan takarar majalisar wakilai ta kasa a PDO ne ya kashe zaben da aka gudanar
- A baya, sanata Aliyu Wamakko ya sake samun nasarar komawa kujerarsa ta sanata a Sokoto ta Arewa
- A jihar Yobe, dan takarar APC, Ibrahim Bomai ya samu nasarar zama sanata a zaben da aka kammala
Jihar Sokoto - Hukumar zabe mai zaman kanta (INEC) ta alanta dan takarar PDP, Abdulssamad Dasuki a matsayin wanda ya lashe kujerar dan majalisa a mazabar Kebbe/Tambuwal a Sokoto.
Wannan na fitowa ne daga bakin baturen zabe, Farfesa Abubakar Sidiq Muhammad, kamar yadda jaridar Tribune Online ta ruwaito.
A cewarsa, dan takarar na PDP ta yi nasara ne da kuri’u 47,317, inda ya lallasa abokin hamayyarsa na APC, Kokani Bala Kebbi mai kuri’u 34,282.
Idan baku manta ba, Dasuki ya kasance dan majalisar wakilai na tarayya a mazabar tsakanin 2015 zuwa 2019 kafin Kokani ya kwace kujerar a 2019.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
A halin da ake ciki, tsohon kwamishinan kudin jihar zai sake komawa majalisa a karo na biyu don maye gurbin Kokani Bala Kebbe.
Tsohon gwamna Wamakko ya lashe zabe
A bangare guda, Aliyu Magatakarda Wamakko ya sake lashe kujerar sanata a karo na uku a jihar Sokoto da ke Arewacin Najeriya.
Wannan na zuwa ne a sakamakon zaben cike gurbi da aka gudanar a jiya Asabar 15 ga watan Afrilu, kamar yadda rahoto ya bayyana.
An ruwaito cewa, Wamakko ya lallasa dan takarar jam'iyyar PDP kuma mataimakin gwamnan jihar a wannan zaben na bana.
A tun farko, an dakata da tattara sakamakon zaben majalisar dokokin tarayya a Sokoto saboda matsalolin tsaro da aka samu.
Ibrahim Bomai ya zama sanata a Yobe
A wani labarin kuma, kun ji yadda dan takarar APC na sanata a mazabar Yobe ta Kudu ya lashe zaben bana.
An sanar da Ibrahim Bomai ne ya lashe yawan kuri'un da aka kada a zaben da aka yi ranar 25 ga watan Faburairu da kuma 15 ga watan Afrilu.
Jam'iyyar APC na ci gaba da samun kujerun siyasa a Najeriya, duk da kuka da ake da ita game da mulkinta na wadannan shekarun.
Asali: Legit.ng