Ado Doguwa Ya Sake Lashe Zabe, Zai Koma Majalisa Salin-Alin a Karo Na Biyar
- Honarabul Ado Doguwa ya sake komawa kujerarsa ta majalisa a karo na biyar bayan sanar da sakamakon zaben da aka karasa a jihar Kano
- An dakatar da ci gaba da zaben Kano saboda wasu matsalolin tsaro da suka dumfaro a yankin Tudun Wada na jihar
- Za a rantsar da majalisa ta 10 a Najeriya a cikin watan Yunin da ke tafe, ciki har da Alhassan Ado Doguwa
Jihar Kano - Shugaban masu rinjaye a majalisar wakilai ta kasa, Alhassan Ado Doguwa ya sake lashe zabe a mazabarsa ta Doguwa/Tudun Wada a jihar Kano.
Wannan na fitowa ne daga bakin wakilin INEC, Sani Ibrahim a lokacin da yake sanar da sakamakon cikon zaben ranar Asabar 15 ga watan Afrilu.
A cewarsa, Doguwa ya samu kuri’u 41,573, inda ya lallasa abokin hamayyarsa na PDP, Yushau Salisu na NNPP da ya samu kuri’u 34,831 a zaben.
Yadda zaben ya kasance
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
A cewar rahoton jaridar Punch, an yi cikon zaben ne a gundumomi takwas na karamar hukumar Tudun Wada a jihar ta Kano da ke Arewa maso Yammacin Najeriya.
A tun farko, hukumar zabe mai zaman kanta (INEC) ta alanta Doguwa a matsayin wanda ya lashe zaben mazabar a ranar 25 ga watan Faburairu, amma daga baya ya soke shi.
An smau rahotanni a yankin Tudun Wada da ke nuna yadda aka samu tsaiko a wasu rumfunan zabe a wancan lokacin, wanda hakan yasa INEC ta sake duba ga sakamakon zaben.
A wancan lokacin da aka soke ayyana sakamakon zaben, Doguwa ya yi nasara ne da kuri’u 38,732, inda Salisu kuwa ke da kuri’u 34,798, rahoton Leadership.
Wannan na nufin, za a rantsar da Doguwa a karo na biyar zuwa majalisa ta 10 da za a rantsar a watan Yunin bana.
Wamakko ya sako komawa kujerarsa a karo na uku
A wani laabrin, kun ji yadda sakamakon zaben sanatan jihar Sokoto ya kasance, inda Aliyu Magatakarda Wamakko ya sake lashe zabe.
Wannan na zuwa ne a cikon zaben da aka gudanar a ranar Asabar 15 ga watan Afrilu, inda aka sanar da wadanda suka lashe zaben.
Wannan na nuni da cewa, Wamakko zai sake komawa majalisar dattawa ne a karo na biyar bayan lallasa abokin hamayyarsa.
Asali: Legit.ng