Wamakko Ya Lallasa Mataimakin Gwamnan Sokoto, Ya Sake Komawa Kujerarsa Ta Sanata
- Rahotanni sun bayyana cewa, Aliyu Magatakarda Wamakko ya sake komawa kujerarsa ta sanatan Sokoto ta Arewa
- A baya, an dakatar da zaben jihar, inda aka ci gaba da yin zaben a ranar 15 ga watan Afrilun da muke ciki
- Ya zuwa yanzu, wannan ne karo na uku da Wamakko zai koma majalisa, kuma ya kasance tsohon gwamnan jihar ta Sokoto
Jihar Sokoto - Tsohon gwamnan jihar Sokoto kuma dan takarar jam’iyyar APC Aliyu Wamakko ne ya lashe zaben sanata a mazabar Sokoto ta Arewa, Punch ta ruwaito.
Wamakko ya lallasa abokin hamayyarsa ne, wanda yake mataimakin gwamnan jihar, Manir Muhammad Dan’Iya na jam’iyyar PDP da tazarar kuri’u 23,023.
Da yake sanar da sakamakon zaben jihar da safe, baturen zabe Ibrahim Magawata ya ce, cikon zaben ya nuna Wamakko ne ya lashe shi da kuri’u 141,468.
Mataimakin gwamnan kuwa, ya samu kuri’u 118,445, kamar yadda jaridar Punch ya ruwaito.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Siyasar Wamakko a jihar Sokoto
Da wannan nasarar da ya samu, Wamakko zai sake komawa majalisar dattawa ne a karo na uku kenan, PM News ta tattaro.
Shi kansa Wamakko ya kasance mataimakin gwamna a tsakanin 1999 zuwa 2006 a karkashin mulkin Attahiru Bafarawa kafin daga bisani ya yi murabus biyo bayan samun sabanin siyasa.
Hakazalika, ya yi gwamna a jihar Sokoto duk da matsaloli da aka samu har ta kai ga an je kotu a lokuta mabambanta game da kasancewarsa dan PDP ko ANPP.
Jihar Sokoto dai na daya daga jihohin da ke yawan daukar hankalin siyasar Najeriya, a wannan shekarar na bata sauya zane ba.
Ibrahim Bomai ya lashe kujerar sanatan Yobe
A wani labarin kuma, kun ji yadda dan takarar sanata a jam'iyyar APC, Ibrahim Bomai ya zama sanatan Yobe ta Kudu a cikon zaben da aka gudanar jiya Asabar 15 ga watan Afrilun 2023.
Ya lallasa abokin hamayyarsa na jam'iyyar PDP da kuri'u masu rata, inda wakilin INEC ya ayyana shi a matsayin wanda ya yi nasara.
Jihar Yobe na daya daga jihohin da aka dakatar da ci gaba da kada kuri'u a zaben ranar 25 ga watan Faburairu saboda faruwar wasu matsaloli da ke da alaka da zaben.
Asali: Legit.ng