Kai Tsaye: Cikon Sakamakon Zaben ’Yan Majalisu da Aka Gudanar a Jihar Kano
A yau Asabar, 15 ga watan Afrilu ne aka karasa zaben 'yan majalisun tarayya da aka dakatar a jihar Kano saboda barkewar rikici.
Bayan da jama'a suka fito suka kada kuri'u, sakamakon zabe ya fara fitowa daga yankuna daban-daban.
Ku biyo domin kawo muku cikakken sakamakon zaben daga jihar ta Kano da ke Arewa maso Yammacin Najeriya.
Ado Doguwa ya sake komawa kujerarsa
Shugaban masu rinjaye a majalisar wakilai ta kasa, Alhassan Ado Doguwa ya sha dakyar, inda ya sake komawa kujerarsa ta majalisa daga mazabar Doguwa/Tudun Wada a jihar Kano.
Doguwa ya samu kuri'u 41,573, inda abokin hamayyarsa na NNPP, Yusha'u Salisu ya samu kuri'u 34,831 kacal.
Dan takarar NNPP ya lashe zaben majalisar wakilai ta kasa a Kano
An sanar da dan takarar NNPP, Barista MB Shehu a matsayin wanda ya lashe zaben sanata a mazabar Fagge ta Kano a majalisar wakilai ta kasa.
MB Shehu ya lallasa dan takarar APC, Aminu Sulaiman Goro da ke neman sake komawa kujerar a karo na uku.
A cewar wakilin INEC, MB Shehu ya samu kuri'u 19,024, sai kuma dan takarar Labour, Shaaibu ABubakar da ya samu kuri'u 12,789, yayin da dan takarar APC kuma ya samu kuri'u 8, 669.
Sakamakon zaben cike gurbi da aka yi a jihar Kano ya fara fitowa
Yammata Gabas, Dan Rimi (rumfuna na 01 zuwa 11, na 13 da 23)
APC - 209
NNPP - 02
PDP - 00
LP - 00
Fagge A. Dandali 002
APC - 28
NNPP - 62
PDP -00
LP - 05
Fagge B. Dandali 004
APC - 65
NNPP - 109
PDP - 01
LP - 07
Sabongari East, Riga Primary 001
APC - 19
NNPP - 47
PDP - 00
LP - 08
Sabon Gari
APC - 298
NNPP - 05
PDP - 04
'Yar Yasa
APC - 162
NNPP - 03
PDP - 00
Jan Dutse
APC - 115
NNPP - 01
PDP - 01
Nata'ala 009
APC - 215
NNPP - 0
PDP -02
Karefa 06
APC - 116
NNPP - 02
PDP - 01