Fintiri da Binani: Masani Ya Yi Hasashen Wanda Ka Iya Lashe Zaben Gwamnan Adamawa
- Wani fitaccen masanin harkar siyasa ya bayyana hasashensa game da sakamakon zaben gwamnan jihar Adamawa
- Masanin mai sharhi kan siyasa da tsaro, Dr Abubakar Sani ya ce, jam'iyyar PDP ce za ta iya lashe zaben gwamnan jihar
- Ya bayyana cewa, dalilin hakan shine; akwai yiwuwar al'ada da addini ya yi tasiri kan Aisha Binani, 'yar takarar APC
FCT, Abuja - Fitaccen mai sharhi kan harkokin siyasa kuma mai fafutukar yaki da ta'addanci, Dr Abubakar Sani ya bayyana hasashensa ga sakamakon zaben gwamnan jihar Adamawa.
Dr Sani ya bayyana cewa, 'yar takarar gwamnan APC a jihar ba lallai ta lashe zaben ba har ma ta kai ga tuge gwamna mai ci, Ahmadu Fintiri na PDP.
Ya ce rikicin cikin gida da jam’iyyar APC ta jihar ke fama da shi da kuma yadda al’ummar Arewa ke yi wa mulkin mace kallon bambarakwai, su ne manyan abubuwan da za su yi wa Bainani cikas.
Matsalolin da Binani ka iya fuskanta
Da yake tattaunawa ta musamman da wakilin Legit.ng, Dr Sani, ya ce:
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
“A gaskiya ban ga alamar 'yar takarar jam’iyyar APC za ta ci zabe ba saboda al'adar zamantakewa da ke da alaka da ganin mace ta mulki maza a Arewacin Najeriya a matsayin wani abu bambarakwai.
“Ni dai bani da wata matsala da kan haka, amma gwamna mai ci yana da abubuwa da yawa a bangarensa, damar APC ta lashe zabe 45% ne cikin 100%. Wannan ya faru ne saboda rikicin cikin gida da jam’iyyar APC reshen Adamawa ke ciki."
“Kwarin giwar mutane na karewa kan INEC” – Dr Sani
Da aka tambaye shi ko hukumar zabe ta INEC ta yi daidai wajen dakatar da ci gaba da tattara sakamakon zaben jihar, amma ta amince da sakamakon zaben Kaduna, sai yace:
"Wannan ne yasa jama'a suka fara rasa kwarin gwiwa kan INEC; akwai rudani da yawa game da yadda hukumar ke tafiyar da lamurranta.
"Bai kamata INEC ta ki amince da sakamakon zaben Adamawa ba amma ta amince tare da sanar da na jihar Kaduna. A nan, INEC bata yi daidai ba."
A kwantar da hankali, a jira sakamakon zabe
Sai dai, ya bukaci masu kada kuri'u da masu ruwa da tsaki a harkar zabe da su kwantar da hankali tare da gudun tashin hankali a zabukan da ke gudana.
Ba a jihar Adamawa ne kadai ake yin zaben gwamna ba a wannan rana, ana yin hakan a jihar Kebbi da sauran jihohin da ake zaben 'yan majalisu da sanatoci.
Asali: Legit.ng