Kano: Yan Sanda Sun Cafke Wasu Mutum 3 Bisa Tilasta Wani Almajiri Cin Bahaya Ana Azumi
- Rundunar ƴan sandan jihar Kano sun cafke wasu mutum 3 bisa zargin tilasta wani almajiri cin bahaya
- Mutanen da aka cafken sun zargi almajirin ne da laifin yi mu su kashi a titin unguwar su
- Yanzu haka yaron yana kwance magashiyyan a gadon asibiti sakamakon wahalar da ya sha a hannun su
Jihar Kano - Rundunar ƴan sandan jiɓsr Kano ta cafke wasu mutum 3 a kwatas ɗin Ja'en Makera cikin Sharada a jihar Kano, bisa zargin tilasta wani almajiri mai shekara 13 cin kashin mutum, wanda aka jefar a yankin.
Lamarin ya auku ne a ranar Alhamis bayan mahaifin yaron Mallam Kabiru, wanda ya fito daga garin Kiru ya kai rahoton lamarin ofishin ƴan sanda na Sharada, cewar rahoton Daily Trust
A cewarsa yaronsa ko zama da kan sa baya iya yi, domin mutanen bayan sun tilasta shi cin bahaya har wanka suka yi masa da shi.
DPO na ofishin ƴan sandan, CSO Abdurrahman, ya tura tawagar jami'ai domin bincike kan lamarin inda suka cafke mutum uku.
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
Wani daga cikin malaman makarantar allon da almajirin ya ke ya gayawa Freedom Rediyo cewa mutanen sun zargin yaron ne da tiƙa mu su kashi a unguwa yayin da kuma ba shi bane ya aikata laifin.
A kalamansa:
"Kawai sun ga kashi ne a unguwar su da misalin ƙarfe 9:30pm, sai suka shiga neman wanda yayi shi. Lokacin da yaron ya zo wuce, wata mata ta hango sai kawai tace shine ya yi. Sai ta riƙe shi sannan ta kira sauran mutanen.
"Suna zuwa kawai sai suka fara sanya masa kashin a fuskar sa sannan suka tilasta mai ya ci."
Martanin yan sandan Kano kan tilastawa almajiri cin bahaya
Da aka tuntuɓe shi, kakakin rundunar ƴan sandan jihar Kano, SP Abdullahi Haruna Kiyawa, ya tabbatar da aukuwar lamarin inda ya bayyana cewa mutum ukun da ake zargi suna tsare a hannun hukuma.
Ya ce yayin da yaron ake cigaba da duba lafiyar sa, tuni aka fara gudanar da bincike kan lamarin, rahoton Platinum Post
Rundunar Yan Sanda Ta Sallami Jami’anta Da Ke Ba Wa Rarara Tsaro
A wani labarin na daban kuma, rundunar ƴan sanda ta kori ƴan sanda da ke ba mawaƙi Dauda Kahutu Rarara tsaro.
Rundunar ƴan sandan ta kore su daga aiki ne bayan ta same su da laifin yin sakaci da aikin su da nuna rashin ƙwarewa.
Asali: Legit.ng