Akwai Matsala: An Hasko Jihohin Arewa Da Za Su Iya Samun Karancin Ruwan Sama A Daminan Shekarar 2023
- Jihohin Arewacin Najeriya kusan 8 ne aka hasko za su iya fuskantar matsalar ƙarancin ruwan sama a wannan shekarar
- Kano, Kaduna da Yobe na daga cikin jihohin da ake zaton matsalar ƙarancin ruwan saman za ta shafa
- Akwai kuma yiwuwar samun ambaliyar ruwa a wasu jihohin ƙasar nan wacce ka iya kai ta bara ko ta wuce ta
Abuja - Darekta Janar na hukumar bayar da agajin gaggawa ta ƙasa (NEMA), Mustapha Ahmed, ya bayyana cewa akwai yiwuwar a samu ƙarancin ruwan sama a birnin tarayya Abuja, Kano Kaduna, Yobe, Bauchi da Jigawa a wannan shekarar.
Jaridar Daily Trust ta rahoto cewa shugaban ya bayyana hakan ne jiya a birnin tarayya Abuja.
Ya bayyana cewa ana tsammanin jihohin Bayelsa, Akwa-Ibom, Delta da Cross River su ruwan sama da ya kai ma'aunin 2700mm ko fiye da haka, cewar rahoton The Guardian
Ya ce a cewar rahoton ambaliyar ruwa na 2023 na hukumar Nigeria Hydrological Services Agency (NHSA), ƙananan hukumomi 66 na cikin hadari mai karfi na samun ambaliyar ruwa daga watan Afirilu zuwa Yuni, 148 daga Yuli zuwa Satumba, sannan 100 daga Oktoba da Nuwamba.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Sannan ƙananan hukumomi 41 suna cikin haɗari mai sauki na samun ambaliyar ruwa daga watan Afirilu zuwa Yuni, 199 a watan Yuli zuwa Satumba da 72 a watannin Oktoba da Nuwamba.
Ahmed ya ce a wannan shekarar za a iya samun ambaliyar ruwa kamar ta shekarar bara ko fiye da ita.
A cewarsa:
"Ambaliyar ruwan bara ta janyo asarar rayuka 665 sannan mutum 3,181 suka jikkata a faɗin ƙasar nan. Mutum 4,476,867 abin ya shafa, inda mutum 2,437,411 suka rasa matsugun nan su, kimanin gonaki 944,989 suka lalace sannan gidaje 355,986 suka lalace gabaɗaya ko suka samu illa."
Mutane Sun Boye Kudin Su: Bankuna Sun Koma Ci Yo Bashi Wajen CBN
A wani rahoton na daban kuma, kun ji yadda bankuna suka koma cin bashin biƙiyoyin naira daga wajen babban bankin Najeriya (CBN), domin gudanar da ayyukan su.
Bankunan kasuwancin sun koma ɗaukar wannan matakin bayan halin tilas ɗin suna faɗa a ciki a dalilin yadda mutane suka koma ɓoye kuɗaɗen su a hannun su,maimakon kai ajiya a banki.
Bankunan Access Bank da First Bank na daga cikin bankunan da ke kan gaba wajen ci yo bashin daga hannun CBN.
Asali: Legit.ng