Mutane Sun Boye Kudin Su: Bankuna Sun Koma Ci Yo Bashi Wajen CBN
- Bankunan kasuwanci a Najeriya sun ci yo bashin N240.57bn daga babban bankin Najeriya (CBN)
- Bayanai daga babban bankin sun nuna cewa waɗannan bankunan sun ci yo bashin sama da N240bn domin gudanar da ayyukan su
- Bankunan suna ciyo bashin ne daga CBN ta hanyar Standing Lending Facility (SLF) wani ma'auni na ƙayyade kuɗin ruwa
Bankunan kasuwanci da suka haɗa da Access Bank, First Bank, da United Bank of Africa, sun yi amfani da tsarin babban bankin Najeriya na Standing Lending Facility (SLF) domin samun kuɗaɗen cigaba da ayyukan su.
Tsarin 'standing lending facility' wani tsari ne wanda manyan bankuna suke ba bankunan kasuwanci da ke fama da matsalar kuɗi ta wucin gadi, bashi na ɗan ƙaramin lokaci.
Hakan yana bayar da dama bankunan su yi amfani da kuɗaden su wajen wasu harkokin, sannan su cike giɓin da suka samu a ƙarshen kowace rana.
A cewar bayanan da aka samu daga CBN, bashin da bankunan suka ci ta hanyar SLF ya kai N240.57bn ya zuwa ranar Laraba, 11 ga watan Afirilun 2023.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Wannan adadin ya zarce da kaso 204.71% kan bashin N78.95bn da bankunan suka ci ya zuwa 12 ga watan Disamban 2022, cewar rahoton Businessday
Dalilin da yasa bankuna ke cin bashi
Ƙaruwar cin bashi ta hanyar SLF bai rasa alaƙa da sauyin fasalin kuɗi da akayi, wanda ya sanya aka samu ƙarancin kuɗi domin kwastomomin bankuna sun ajiye kuɗaɗen su a gida a maimakon su kai su bankuna.
Babban bankin CBN a ranar 25 ga watan Oktoban 2022 ya sanar da cewa zai sauya fasalin N200, N500, da N1,000 sannan za su daina yawo daga ranar 15 ga watan Disamban 2022. Bankin ya umurci bankuna da su kai tsaffin kuɗin da ke hannun su zuwa CBN.
Kwashe tsaffin kuɗin da CBN yayi daga wajen bankuna ya taimaka wajen ƙalubalen da bankunan suka fuskanta.
Bankuna suna buƙatar tsabar kuɗi domin gudanar da ayyukan su, tun daga kan biyan kwastomomin su, bayar da bashi, zuba jari da sauran su.
Neman Magajin Emefiele Ya Yi Nisa, An Hasko Wasu Manyan Mutane Da Tinubu Zai Iya Ba Mukamin
A wani labarin na daban kuma, Tinubu ya fara neman wanda zai gaji kujerar Godwin Emefiele ta gwamnan babban bankin Najeriya (CBN).
Akwai wasu manyan mutane da ake hasashen daga cikin su Tinubu zai ɗauki ɗaya ya miƙa masa rahamar shugabancin CBN.
Asali: Legit.ng