Gwamnatin Buhari Ta Bayyana Adadin 'Yan Najeriya Da Ta Tsamo Daga Kangin Talauci a 2022

Gwamnatin Buhari Ta Bayyana Adadin 'Yan Najeriya Da Ta Tsamo Daga Kangin Talauci a 2022

  • Gwamnatin Tarayya ta ce ta samo ƴan Najeriya sama da mutum miliyan 2 cikin ƙangin talauci a shekarar 2022
  • Wani sabon rahoto da aka fitar ya yi bayani filla-filla kan yadda ƴan Najeriya da dama suka amfana
  • Gwamnatin ta kawo shirye-shirye da dama domin tsamo ƴan Najeriya cikin ƙangin talauci

Abuja - Wani rahoto ya bayyana cewa sama da ƴan Najeriya mutum miliyan biyu ne masu fama da tsananin talauci suka amfana da shirin gwamnatin tarayya na rage talauci a ƙasa a turance National Poverty Reduction with Growth Strategy (NPRGS) a shekarar 2022.

Hadimin mataimakin shugaban ƙasa a fannin watsa labarai, Laolu Akande, a wata sanarwa ranar Alhamis ya ce shugabannin kwamitin NPRGS sun gudanar da taro a fadar shugaban ƙasa, a birnin tarayya Abuja, cewar rahoton Premium Times

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: 'Yan Bindiga Sun Sake Kai Kazamin Hari a Watan Azumi, Sun Kashe Mutane a Arewa

Gwamnatin Buhari ta tsamo 'yan Najeriya 2m daga talauci
Hotunan wasu 'yan Najeriya na zirga-zirga a kasuwa Hoto: Premiumtimes.com
Asali: UGC

Mr Akande yace rahoton da aka gabatar a taron wanda mataimakin shugaban ƙasa, Farfesa Yemi Osinbajo, ya jagoranta, ya nuna cewa ƙananan manoma miliyan 1.6 ne suka amfana da tallafin noma.

Bayan nan, matasa 13,000 sun samu horarwa kan koyon sana'o'i a jihohi 6 da suka haɗa da Legas, Ogun, Enugu, Gombe, Kaduna da Nasarawa, yayin da shirye-shirye sun yi nisa don horar da 2000 a jihar Edo.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

“Haka kuma, sama da ƴan Najeriya 8,000 aka ɗauka aikin gina hanyoyin karkara a ƙarƙashin shirin gina hanyoyin karkasa, wanda aka gina hanyoyi 40 cikin ƙauyuka 120, wanda tsawon su ya kai kilomita 57.3 a faɗin ƙasar nan."

The Guardian ta ce rahoton wanda ƙaramin ministan kasafin kuɗi da tsare-tsare, Clem Agba, ya gabatar ya nuna cewa bayan an sako N50bn an kammala wasu muhimman ayyuka.

Kara karanta wannan

Neman Magajin Emefiele Ya Yi Nisa, An Hasko Wasu Manyan Mutane Da Tinubu Zai Iya Ba Mukamin

Ayyukan da aka samu nasarar kammala wa ɗari bisa ɗari sun haɗa da shirin noma don abinci da samar da aikin yi, Agriculture for Food and Jobs Plan (AFJP), aikin gina hanyoyin karkara, da sauran su.

“Adadin yawan mutanen da suka amfana da shirye-shiryen yanzu haka ya kao 1.8m sannan kuma an ɗauki mutum 9,527 domin gudanar da ayyukan."
"Haka kuma, a wajen taron kwamitin ya amince da fitar da N250bn domin gudanar da ayyukan shekarar 2023."

Yara Miliyan 17 Ke Fama Da Tamowa a Najeriya", Gwamnatin Tarayya

A rahoton na daban kuma, gwamnatin tarayya ta bayyana adadin yaran da ke fama da matsalar rashin abinci mai gina jiki a ƙasar nan.

Gwamnatin ta ce matsalar tamowa na ƙara ƙaruwa a ƙasar nan.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng