Kyakkyawar Fahimtar Addinin Musulunci Shi Ne Mabudin Zaman Lafiya Ga Duniya, Buhari
- Shugaba Buhari ya bayyana cewa koyarwar addinin musulunci ce hanyar kawo zaman lafiya ga duniya
- Shugaban ya bayyana haka ne a ziyarar da ya kai birnin Madinah da ke kasar Saudiyya, yayin da ya ke zagaya wuraren tarihin musulunci
- Shugaban ya kuma bayyana cewa akwai aiki a gaban musulmin duniya wajen fahimtar hakikanin addinin musulunci ba tare da sabanin fahimta ba
Shugaba Muhammadu Buhari ya ce dole ne a samu kyakkyawar fahimtar musulunci, a jingine bambancin fahimta, a matsayin hanyar da za a tabbatar da zaman lafiya ga duniya, kwanciyar hankali da cigaba.
Ya bayyana haka jiya Madinah, kasar Saudiyya, lokacin da ya ke magana bayan ziyarar da kai gidan adana kayan tarihin annabi SAW da cibiyar wayar da kan musulmi a birnin a wani bangare na ziyarar da kai birnin mai alfarma.
Yadda ainihin koyarwar addinin musulunci shine babban aikin da ke gaban musulmi - Buhari
Buhari, cikin wata sanarwa da mai magana da yawunsa, Garba Shehu ya fitar, ya ce yada ainihin ilimin addinin musulunci shi ne babban aikin da ke gaban musulmin duniya.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ya yabawa gwamnatin Saudiyya kan yadda ta samar da na'urorin zamani don cigaban musulunci, manufofinsa da abin da ya ke koyarwa.
Ya ce al'ummar musulmi na bukatar hanya mai sauki "don samun ilimi a zamanance don fahimtar abin da addinin."
Ya yabawa hukumomin Saudiyya bisa kokarin su na wayar da kan duniya game addinin musulunci, sai dai ya ce har yanzu akwai bukatar sauran kasashe su zage damtse.
Ya ce gidan adana tarihin ''na kokarin adanawa tare da fito da ainihin addinin musulunci, da kyawawan abubuwan da ya ke koyarwa, da sakon na jinkai, soyayya, adalci, zaman lafiya, da daidaito, ta hanyar abubuwan al'ada da gidajen tarihin da ke fito da kyawawan gine-gine da alfarma.
"Ta kuma samar da gamsassun kayan tarihin annabi, kyakkyawan halinsa, dabi'unsa, da kuma koyarwarsa, ta hanyoyin kimiyya, samar da kayan kimiyyar zamani don taimakawa masu bincike, ta hanyar amfani da kayan kimiyyar zamani mafiya inganci."
Buhari Zai Tafi Saudiyya Ziyara, Zai Yi Aikin Umrah
Tunda farko kun ji cewa Shugaban na Najeriya Muhammadu Buhari, a ranar Talata ya baro Abuja ya kama hanyar zuwa kasar Saudiyya inda ake fatan zai shafe kwanaki takwas.
A yayin ziyarar da Buhari zai kai kasa mai tsarkin a matsayinsa na Shugaban Kasa, ana sa ran zai samu damar yin aikin Ibada na Umrah.
Babban hadimin shugaba Buhari a bangaren watsa labarai, Garba Shehu, ya sanar da hakan.
Asali: Legit.ng