Neman Magajin Emefiele Ya Yi Nisa, An Hasko Wasu Manyan Mutane Da Tinubu Zai Iya Ba Mukamin
- Zaɓaɓɓen shugaban ƙasa, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu, ya fara neman sabon gwamnan CBN
- Rahotannin sun ce manyan ƙusoshi a fannin banki da wani sabon tsohon gwamnan CBN na cikin jerin waɗanda Tinubu ke dubawa
- Duk da cewa gwamnan CBN na yanzu, Godwin Emefiele, yana da sauran shekara 1, masu sharhi sun Tinubu korar sa zai yi
Abuja - A cewar rahotanni zaɓaɓɓen shugaban ƙasa, Bola Tinubu da hadimansa sun fara neman wanda zai gaji gwamnan babban bankin Najeriya (CBN), Godwin Emefiele.
Tinubu da tawagar sa suna ta haɗa jerin mutanen da za su ba manyan muƙamin a cikin sabuwar gwamnati wacce za a rantsar da ita a ranar 29, ga watan Mayun 2023, cewar rahoton BusinessDay.
Rahotan ya bayyana cewa neman wanda zai shugabanci babban bankin Najeriyan yana da matuƙar muhimmanci wanda ake so da gaggawa, saboda tsamo ƙasar nan daga cikin koma bayan tattalin arziƙin da ta ke samu cikin hanzari.
Dole ne dai neman magajin Emefiele da ake yi ya samar da ƙwararren masani a fannin mace ko namiji wanda aka amince ya cigaba da tafiyar da ragamar babban bankin na CBN.
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
Wadanda ake duba yiwuwar ba su mukamin babban bankin Najeriya, CBN, karkashin gwamnatin Tinubu
A rahoton jaridar, waɗanda ake duba yiwuwar ba su muƙamin sun haɗa da:
1. Fola Adeola, shugaban bankin Guaranty Trust Bank kuma wanda ya assasa fannin fansho na zamani.
2. Bode Agusto, tsohon darekta a ofishin ƙasafin kuɗi na tarayya wanda ya ke da digiri a fannin accounting daga Legas da satifiket a fannin strategy and innovation daga MIT.
3. Oluyemi Cardoso, tsohon shugaban bankin Citi Bank kuma tsohon kwamishinan cigaban tattalin arziƙi na jihar Legas a gwamnatin Tinubu. Yana da digiri daga jami'o'in Aston da Havard.
4. Olawale Edun, tsohon kwamishinan kuɗi na jihar Legas a gwamnatin Tinubu.
Akwai Yiwuwar Sanusi II Ya Dawo Bankin CBN a Matsayin Gwamna a Mulkin Tinubu
A wani rahoton kun ji cewa akwai yiwuwar tsohon gwamnan babban bankin Najeriya, Sanusi Lamido Sanusi II, yayi kome kan kujerar sa ta shugabancin babban bankin.
Rahotannin sun hasko cewa Tinubu yana duba yiwuwar dawo da tsohon sarkin na Kano kan wannan babbar kujera.
Asali: Legit.ng