“Ke Ki Shiga”: Matar Aure Da Uwar Mijinta Sun Fafata Kan Wanda Zai Zauna a Gaban Mota a Bidiyo

“Ke Ki Shiga”: Matar Aure Da Uwar Mijinta Sun Fafata Kan Wanda Zai Zauna a Gaban Mota a Bidiyo

  • Wani mutumi ya zuba ido cike da sha’awa yana kallon yadda mahaifiyarsa da matarsa ke muhawara kan wanda zai zauna a gaban motarsa
  • Su dukka biyun sun ki yarda da shawarar, yayin da matar ta dage cewa ba za ta zauna a gaban motar ba
  • Bidiyon da ya yadu a soshiyal midiya ya haifar da cece-kuke a tsakanin jama’a kan dabi’ar matar da uwar mijin

Wani mutumi ya yada wani bidiyo da ke nuna yadda mahaifiyarsa da matarsa suka yi kaca-kaca da matsalar nan na wanda zai zauna a gaban motarsa.

Su dukka ukun sun shirya don fita unguwa lokacin da yar dirama ta kaure a tsakanin matar da mahaifiyar tasa.

Uwar miji da sukarta wajen shiga mota
“Ke Ki Shiga”: Matar Aure Da Uwar Mijinta Sun Fafata Kan Wanda Zai Zauna a Gaban Mota a Bidiyo Hoto: @nypost Source: TikTok
Asali: TikTok

Matarsa ta zauna a kujerar baya, tana mai umartan uwar mijinta da ta zauna a kujerar gaba amma matar ta ki amsa tayin.

Kara karanta wannan

Tir da talauci: An kirkiri motar da mutum zai iya kiranta a waya, kuma ta zo babu direba

Ta nace cewa lallai sai dai uwar mijin ta karbi wannan karramawar, kuma bayan matar dan nata ta nace a kan hakan, sai matar ta zauna a gefen danta a cikin motar.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Da yake martani ga bidiyon, Nathan ya rubuta:

“Wannan kujerar gaban ya haddasa matsala iri-iri a tsakanin mata da iyayen mazajensu da dama. Ban san menene a cikin kujerar gaban nan ba.”

Kalli bidiyon a kasa:

Jama’a sun yi martani a soshiyal midiya

Jozzy ya ce:

“Dole mata masu karfi su dunga nuna soyayya kuma hakan zai sa a dunga ganin mutuncinki a gidan aurenki na jiniinawa matarka.”

Jangmi ta ce:

“Ganin mutuncin juna na da matukar amfani, kakar ya ki amsa tayin da farko maimakon shiga kujerar gaba kai tsaye. Dangantaka irin wannan na da kyau.”

Kara karanta wannan

“Za Mu Iya Kebewa?” Matashi Ya Hangi Kyakkyawar Budurwa a Gefen Mahaifiyarta, Ya Mika Mata Wasikar Soyayya

_jessicajiachim ta ce:

“Haka yakamata ya kasance. Kuma duk ranar da ni a matsayin mata na yanke shawarar zama a gaba, kada a kalle shi a matsayin matsala. Fahimta.”

ousmanajobe ya ce:

“Allah ya kare wannan matar da aurenta daga idon makiya, Allah ya barsu tare cikin zaman lafiya da soyayya har abada.”

Wata kwararriyar mai bayar da shawarwari kan abun da suka shafi aure, Malama Binta Kuta ta yi martani a kan gishirin zaman lafiya tsakanin uwar miji da matar da.

Malama Binta ta ce yawanci ana samun matsala ne idan uwar miji ta zamo mai sanya idanu a kan gidan danta sannan kuma idan aka yi rashin dace da matar da mara tarbiya.

Ta ce:

"Idan har ke uwa za ki kame kanki sannan ki tsaya a matsayin na uwar miji kuma ki dauki surukar taki da zuciya daya kamar ke kika haifeta, toh za ki ga duk rashin tarbiyarta za ta sarara maki.

Kara karanta wannan

Hakimin mata: Mata ta gano mijinta zai kara aure, ta yashe kudin asusun hadin gwiwarsu

"Kamar wannan uwa da ake magana a kanta, kin ga bata za'ke ta ce ita ai motar danta bane sai ta zauna a gaba, ita kuma matar 'dan an yi dace ta san yakamata, da za ki bi diddigin zamansu za ki ga cewa surukar na matukar kaunarta, sannan ta dauketa kamar diyarta shiyasa har zaman nasu ya zama haka."

Wata mata ta bingire da bacci tana tsaka da tuki, motar ta ci gaba da tuka kanta

A wani labarin kuma, jama'a sun cika da mamaki bayan cin karo da bidiyon wata mata da ke bacci yayin da take tsaka da tuka motarta kirar Tesla. Motar ta ci gaba da tuka kanta ba tare da matsala ba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng