Dogon Gini Mai Hawa Bakwai Ya Danne Ma'aikata a Jihar Legas

Dogon Gini Mai Hawa Bakwai Ya Danne Ma'aikata a Jihar Legas

  • Gini mai hawa Bakwai ya rushe a yankin Banana Island a jihar Legas, ma'aikatan da ke aiki a wurin sun maƙale
  • Shugaban hukumar NEMA reshen jihar ya tabbatar da kifewar ginin, ya ce tuni suka shirya jami'an agaji zuwa wurin
  • Kwamishinan tsara birane na Legas ya ziyarci wurin domin gane wa idonsa kuma ya kaddamar da fara bincike

Lagos - Bene mai hawa Bakwai da ake kan aikin ginawa a Anguwar Banana Island a jihar Legas ya rushe kuma ma'aikata da yawa sun maƙale a ciki.

Daily Trust ta tattaro cewa zuwa yanzun jami'an kai Agajin gaggawa da dama sun mamaye wurin da ginin ya kife domin kaiwa mutanen da suka maƙale ɗauki.

Bene ya rushe.
Benen da ya rushe a Banana Island Hoto: thenation
Asali: UGC

Wata majiya ta ce duk da babu tabbacin abinda ya kawo rushewar ginin, amma ma'aikata na cikin aikin zuba Kankare a hawa na shiga gabanin aukuwar lamarin.

Kara karanta wannan

Jirgin Yaƙin Soji Ya Kai Ɗauki Yayin da Yan Bindiga Suka Kaiwa Mutane Hari da Azumi, Da Yawa Sun Mutu

Wane mataki aka ɗauka?

Shugaban hukumar ba da agajin gaggawa ta ƙasa reshen jihar Legas (NEMA) ya tabbatar da faruwar lamarin a wani takaitaccen bayani da yammacin ranar Laraba.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

"Mun samu rahoton rushewar ginin bene a Banana Island, ma'aikata sun maƙale a ciki, muna kokarin haɗa jami'an da zasu kai ɗauki," inji shi, kamar yadda The Nation ta rahoto.

Ginin ba kan ƙa'ida yake ba

Da yake tsokaci kan abinda ya faru, mataimakin Darektan sashin yaɗa labarai na ma'aikatar tsare-tsare da raya birane, Mukaila Sanusi, ya ce, "Haramtaccen bene mai hawa 7 da ake kan ginawa ya ruguje."

Ya ce, "Mutanen da suka ji raunuka an fara musu magani, babu wanda ya mutu sakamakom lamarin. Wannan ibtila'i ya auku ne bayan zuba kankare."

"Kwamishinan tsare-tsare da raya birane na jiha, Tayo Bamgbose-Martins, ya ziyarci wurin da benen ya faɗo domin ganin halin da ake ciki da kuma fara bincike."

Kara karanta wannan

Lambar Ministoci 2 Ya Fito da ‘Yan Majalisa Ke Binciken Satar Gangunan Mai Miliyan 48

Legit.ng Hausa ta fahimci cewa wannan ne rushewar bene na baya-bayan nan a jerin matsalar rugujewar gine-ginen da ake fama da ita a jihar Legas cikin shekarun nan.

A wani labarin kuma Babbar Kotu Ta Kara Hargitsa PDP, Ta Kori Shugabannin Jam'iyya a Jihar Katsina

Lamarin ya ƙara dagulawa jam'iyyar PDP lissafi yayin da take kokarin shawo kan rigingimun da suka hana ta zaman lafiya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262

Tags:
Online view pixel