Matashiya Ta Bige Da Bacci Yayin Da Take Tsaka Da Tuka Motarta Kirar Tesla
- Wata matashiyar mata wacce ke tuka motar Tesla yayin da take bacci ta yi fice a dandalin TikTok
- A bidiyon wanda ya yadu a soshiyal midiya, an gano matar tana sharbar bacci amma motar ta ci gaba da tafiya a titi ba tare da tangarda ba
- A daidai lokacin kawo wannan rahoton, bidiyon ya tara 'likes' fiye da 300,000 da martani fiye da 2000 a TikTok
Wata mata da ta mallaki wata sabuwar mota daga kamfanin Tesla ta kama sharar bacci yayin da take tuki amma kuma motar bata yi tawo mu gama da wata ba duk da cewar ta ci gaba da tafiyarta.
Bidiyon da ya yadu wanda wani mutum da ke tuki a hanyar ya dauka ya nuna lokacin da matar ta bingire da bacci a motar kirar Tesla.
Guntun Gatarinka Ya Fi Sari Ka Bani: Matashi Ya Gaji Da Biyan Kudin Haya, Ya Gina Daki 1 a Kan Filinsa a Bidiyo
Mota mai tuka kanta
Duk da cewar akwai motoci da dama a hanyar, ita motar bata haddasa hatsari ba domin dai tana ta tuka kanta ne kai tsaye.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Mabiya shafukan soshiyal midiya da dama da suka ga bidiyon sun cika da mamakin motar wacce ke nuna ci gaban da aka samu a fasahance.
Kalli bidiyon wanda @nypost ya wallafa a kasa:
Jama'a sun yi martani
@Llonelhernandez ta yi martani:
"Wannan shine amfanin mallakar motar Tesla lol."
@BoMmL ya ce:
"Mu yi magana ta gaskiya mun yarda da tukin Tesla foiye da tukin yawancin mutane."
@Vasllst ya rubuta:
"Takardar sharadin tuki na Tesla ya bayyana cewa ka kula koda yana tuka kansa."
@Kevinh ya yi martani:
"Ina da wata abokiya da ta fada mani cewa sun je shan barasa sai na tambaya wa ya kawo ku gida. Ta ce Tesla.
@felicia3637 ta ce:
"Tana tuki fiye da kai da kake kan wayan nan."
Matashiya ya gwangwaje kansa da motar miliyan N160
A wani labarin kuma, mutane a soshiyal midiya sun cika da mamaki bayan cin karo da bidiyon wani matashi da ya gwangwaje kansa da mota kirar Rolls Royce da kudinta ya kai miliyan 160.
Matashiya ya shiga cikin motar sannan ya hasko yadda cikinta yake inda mutane ke ta santi tare da fatan Allah ya mallaka masu irinta.
Asali: Legit.ng