Kotu Ta Soke Tarukan Jam’iyyar APC Na Kogi Na Zabo Dan Takarar Gwamna
- Kotu ta soke zabukan da aka yi na samar da dan takarar gwamnan APC a jihar Kogi saboda wasu dalilai
- Wannan na faru ne bayan da wasu jiga-jigan jam'iyyar suka maka wadanda suka gudanar da tarukan zaben a kotu
- Ya zuwa, kotun ta umarci APC ta gudanar da sahihin taron zabe daidai da kundin zabe da kundin mulkin APC
FCT, Abuja - Wata babbar kotun tarayya da ke zamanta a Abuja ta soke tarukan gundumomi da na kananan hukumomi da aka ce jam’iyyar APC ta gudanar a ranar 7 ga watan Fabrairu a Kogi domin samar da dan takararta a zaben gwamna da za a yi a watan Nuwamba.
A tun farko, wasu mambobin jam’iyyar APC a karkashin jagorancin Realwan Okpanachi sun garzaya kotu domin neman a soke zabukan biyu da aka gudanar a jihar, Tribune Online ta ruwaito.
Da yake yanke hukunci a ranar Laraba, Mai shari’a James Omotosho ya haramtawa hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa (INEC) yin amfani da jerin sunayen deleget-deleget da jam’iyyar ta fitar daga tarukan don tsayar da dan takarar gwamna.
Dalilin soke taron da aka yi
Kotun ta soke tarukan ne saboda ba a gudanar da su daidai da yadda dokar zabe ta 2022 da kuma kundin tsarin mulkin jam’iyyar APC suka tanada ba.
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
Hakazalika mai shari’a Omotosho ya bayyana cewa jam’iyyar APC ta kasa fitar da takardar sakamakon zaben domin nuna adadin kuri'un da mahalarta taron sun kada a gundumomi da kananan hukumomin.
Ba wannan ne karon farko da ake samun matsalar da ke kai wa ga soke zaben fidda gwani ko shirinsa ba a Najeriya, Channels Tv ta ruwaito.
Don haka kotun ta umurci jam’iyyar APC da ta gudanar da taro na musamman na gunduma da kananan hukumomi bisa tanadin dokokin da suka dace, musamman sashe na 84 na dokar zabe da sashe na 13 na kundin tsarin mulkin APC.
A baya kun ji yadda majalisar dokokin jihar Kano ta amince da bukatar gwamna Abdullahi Umar Ganduje na gyara ga masarautun jihar Kano da ke Arewa maso Yammacin Najeriya.
Asali: Legit.ng