Majalisar Borno: Zababben Dan Majalisa Mai Wakiltar Mazabar Chibok Ya Rasu a India
- Allah ya yi wa zababban dan majalisa mai wakiltar mazabar Chibok a majalisar dokokin jihar Borno, Nuhu Clark, rasuwa
- Clark ya kwanta dama a ranar Litinin, 10 ga watan Afrilu a kasar Indiya inda ya je yin jinya
- Kwamishinan harkokin cikin gida, labarai da al'adu na jihar, Babakura Abbajatau, ya tabbatar da rasuwar dan siyasar
Borno - Labari da ke zuwa mana a yanzu shine cewa zababban dan majalisa mai wakiltar mazabar Chibok a majalisar dokokin jihar Borno, Nuhu Clark ya mutu, Aminiya ta rahoto.
Mista Clark ya rasu ne yayin da yake jinya a kasar Indiya a ranar Litinin, 10 ga watan Afrilu.
Kwamishinan harkokin cikin gida, labarai da al'adu na jihar, Babakura Abbajatau, ne ya tabbatar da ci gaban a wata hira da aka yi da shi a ranar Laraba, 12 ga watan Afrilu, a garin Maiduguri, babban birnin jihar Borno Peoples Gazette ta rahoto.
Gwamnati za ta fitar da sanarwa a hukumance, Abbajatau
Mista Abbajatau ya ce gwamnatin jihar za ta fitar da sanarwa a hukumance nan ba da jimawa ba bayan ta zanta da iyalan mamacin.
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
Yayin da yake jimamin mutuwar marigayin, mataimakin gwamna Umar Kadafur ya bayyana mutuwar a matsayin babban rashi ga iyalansa, mutanen kudancin Borno da jihar baki daya.
Mista Kadafur ya bayyana mutuwar a matsayin babban rashi ga jam'iyyar All Progressives Congress (APC), duba ga gagarumin rawar ganin da ya taka wajen ci gaban Borno.
Ya yi ta'aziyya ga iyalan marigayi dan siyasan sannan ya roki Allah ya baiwa danginsa hakurin jure wannan rashi da suka yi.
Mista Clark ya kasance tsohon kwamishinan yaki da talauci kafin ya yi murabus a ranar 25 ga watan Afrilun 2022 don yin takarar kujerar dan majalisa mai wakiltan mazabar Chibok karkashin inuwar APC.
PDP ba za ta ci zabe ba idan ta bai wa Dino tikitin takarar gwamnan Kogi, Wike
A wani labari na daban, gwamnan jihar Ribas, Nyesom Wike ya gargadi jam'iyyar PDP a kan mika tikitinta na takarar gwamnan jihar Kogi ga Sanata Dino Melaye.
A cewar Wike, Dino mai da cancantar da ake bukata daga wajen wani da zai shugabanci jiha a matsayin gwamna.
Asali: Legit.ng