Jami'an NDLEA Sun Cafke Wata Tsohuwa Mai Safarar Miyagun Kwayoyi a Jihar Rivers
- Wata tsohuwa mai safarar miyagun ƙwayoyi a jihar Rivers ta faɗa komar jami'an hukumar NDLEA
- Jami'an hukumar sun cafke tsohuwar ne tana ɗauke da miyagun ƙwayoyi na miliyoyin naira
- Tsohuwar ta shiga hannu ne a wani sumame da jami'an hukumar suka kai bayan sun samu baya nan sirri
Jihar Rivers- Jami'an hukumar hana sha da fataucin miyagun ƙwayoyi (NDLEA) a jihar Rivers sun cafke wata mata mai shekara 65 a duniya, wacce ake zargin dillaliyar miyagun ƙwayoyi ce.
Jaridar Vanguard ta rahoto cewa jami'an sun kuma ƙwace miyagun ƙwayoyi waɗanda kuɗin su ya kai N4m a hannun matar.
Matar mai suna Angela Sunday, ta shiga hannun jami'an hukumar ne a ƙauyen Odagwa cikin ƙaramar hukumar Etche ta jihar Rivers.
An samu matar tana ɗauke da miyagun ƙwayoyin da suka haɗa da 800grm na methamphetamine, 250grm na tabar wiwi da 59grm waɗanda kuɗin su ya kai N4m.
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
Kakakin hukumar NDLEA ta jihar, Emmanuel Ogbumgbada, ya tabbatar da cafke matar da jami'an hukumar suka yi, cewar rahoton The Guardian
Ogbumgbada a wata sanarwa da ya fitar a birnin Port Harcourt ya ce jami'an hukumar bayan samun bayanan sirri sun dira a wata maɓoyar ɓata gari inda a nan suka cafke Angela Sunday, sannan ya ƙara da cewa an same ta da miyagun ƙwayoyi daban-daban.
A kalamansa:
“A ranar Alhamis, 6 ga watan Afirilun 2023 da misalin ƙarfe 5 na yamma, jami'an NDLEA na jihar Rivers sun kai sumame a Odagwa, cikin ƙaramar hukumar Etche, sannan suka cafke Angela Sunday ɗauke da miyagun ƙwayoyin da kuɗin su ya kai N4m."
El-Rufai Ya Yabama Dakarun Sojoji Kan Kashe Kasurgumin Dan Bindiga
A wani labarin na daban kuma, gwamnan jihar Kaduna, Nasir Ahmed El-Rufai ya yaba da kisan da dakarun sojoji suka yi wa wani ƙasurgumin ɗan bindiga a jihar.
Dakarun sojojin Najeriya sun samu nasarar halaka Isiya Danwasa, wani ƙasurgumin ɗan bindiga wanda ya addabi mutanen jihar Kaduna.
Dakarun sojojin sun samu nasarar halaka ɗan bindigan ne a wani kwanton ɓauna da suka yi masa.
Asali: Legit.ng