Yadda Kwangilar N10bn Ta Yi Silar Rasa Aikin Hadiza Bala Usman a Gwamnatin Buhari

Yadda Kwangilar N10bn Ta Yi Silar Rasa Aikin Hadiza Bala Usman a Gwamnatin Buhari

  • Hadiza Bala Usman ta bada labarin yadda aka zo mata da maganar biyan $22.5m ga wani kamfani
  • NPA ta kafa kwamiti a lokacin, ta gano ashe Niger Global Engr. Ltd bai yi aikin da NPA ta ba shi ba
  • Bayan kin biyan wadannan kudi Bala Usman ta ki yarda ta tsawaita kwangilar kamfanin INTEL

Abuja - Tun bayan barinta ofis a 2021, Hadiza Bala Usman a littafinta, tayi fito da na ta bangaren na abin da ya sa Ministan sufuri ya dakatar da ita.

Jaridar Daily Trust ta ce tsohuwar Manajar hukumar da ke kula da tashoshin Najeriya ta fasa-kwai ne a littafin da ta rubuta game da zamanta a NPA.

Hadiza Bala Usman take cewa kin biyan $22m domin aikin yasar tashar ruwan Kalaba da kuma sabunta kwangilar INTEL ya jefa ta cikin matsala.

Kara karanta wannan

Ku rabu dashi: Peter Obi ya tafi kotu ya shirga karya game da zabe, INEC ta yi martani

Litaffin da aka buga ya yi bayanin yadda a watanni shidan karshenta a kan kujerar hukumar NPA, Hadiza Usman ta fahimci irin rigimar da ta dauko.

Bala Usman ta dauko ruwan dafa kan ta

Jajirtaciyyar matar take cewa ta fahimci irin aika-aikar da ake yi, amma mutum ba zai gane kamarin da lamarin ya yi ba sai ya shigo cikin harkar.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

An rahoto Hadiza ta na cewa yashe tashoshin ruwan da ke sauran garuruwa zai zo da kalubale a dalilin rashin tsaro da matsalar tituna da ake da su.

Littafin ya yi bayanin abin da ya hana hukumar NPA ta yashe tashoshin ruwan Warri, Onne, Fatakwal da Kalaba a lokacin Hadiza Bala tana ofis.

Hajiya Hadiza Bala Usman
Hajiya Hadiza Bala Usman a Ofis Hoto: premiumtimesng.com
Asali: UGC

An nemi a biya bashin $22.5m

Tsohuwar shugabar hukumar ta ce a 2017 ta fara shiga matsala da Ma’aikatar sufuri ta aiko mata takarda a kan aikin kamfanin Niger Global Engr. Ltd.

Kara karanta wannan

Hadiza Bala Usman Ta Rubuta Littafin da Ya Tona Abin da Ya Jawo Amaechi Ya Kore ta a NPA

Lauyoyin kamfanin sun bukaci Ministan sufuri ya sa baki a biya su $22m da suka ce su na bin NPA, Hadiza ta bincika ta ga babu aikin da kamfanin ya yi.

Abin da binciken kwamitin NPA ya nuna a lokacin shi ne kamfanin ya karbi $12.5m, sai aka ki biyan bashin aka kuma nemi su dawo da abin da aka biya su.

...batun kwangilar kamfanin su Atiku

A wani sashe na littafin, Daily Nigerian ta ce an yi maganar kwangilar jiragen ruwan kamfanin Integrated Logistics da gwamnatin tarayya da aka soke.

Bayanin littafin ya nuna kin tsawaita wa’adin kwangilar Intel da shekara guda ya yi sanadin da Rotimi Amaechi ya yi umarni a dakatar da Hadiza Usman.

Littafin Stepping on Toes

A rahoton da muka fitar dazu, an ji Hajiya Hadiza Bala Usman ta bada labarin abin da ya hada ta fada da Mai gidanta a gwamnatin tarayya a shekarar bara.

Kara karanta wannan

Ana Saura Kwanaki 50 Ya Bar Aso Rock, An Yi Karar Shugaba Buhari da NBC a Kotu

A farkon 2022, Rotimi Amaeci ya sa hannu aka kori Bala Usman daga kujerar shugabar NPA, sabon littafinta na “Stepping on Toes' ya zo da bayani.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng