Fasto Ya Kwaikwayi Azumin Annabi Isa Na Kwana 40, Ya Mutu a Kwana Na 25
- Francisco Barajah, wani fasto dan kasar Mozambique ya mutu bayan gwada azumin kwanaki 40 a kokarin yin koyi da Yesu Almasihu
- Ka tuna cewa a cikin littafin Injila, an ruwaito yadda Yesu Almasihu ya azumci kwanaki 40 a cikin daji a can cikin Dutsen Zaitun
- An bayyana cewa, bayan shafe kwanaki 25 bai ci abinci ko ruwan sha ba, faston ya rarrame har ta kai ya kasa tashi kwata-kwata
Mozambique - A wani al'amarin da ya bai wa mutane da dama mamaki a fadin duniya, wani fasto mai suna Francisco Barajah ya rasa ransa sakamakon kwaikwayan tarihin addininsa.
Bawan Allahn ya mutu ne a kasar Mozambique a lokacin ya kuduri yin azumi na kwanaki 40 don yin koyi da tarihin Yesu Almasihu a Dutsen Zaitun na littafin Injila.
BBC ta ruwaito cewa bawan Allahn dan kasar Mozambique na kan azumi na 25 ne kacal daga cikin 40 da ya kudurta yi amma ya sheke.
Barajah, wanda ya assasa cocin Santa Trindade Evangelical a tsakiyar lardin Manica na kasar Mozambique, an tabbatar da mutuwarsa ne a wani asibiti da ke birnin Beira inda ya yi jinya.
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
Yadda azumi ya galabaitar dashi
An ce ya rasa da yawa daga lakar jikinsa har ta kai ya kasa tashi, bai iya ko wanka ko motsi, kuma kokarin taimaka masa ya murmure ya ci tura, Africa News ta tattaro.
‘Yan uwansa da ’yan cocinsa sun kai shi asibiti domin yi masa magani saboda yanayinsa ya yi kamari da kuma yadda yake ci gaba da tabarbarewa da galabaita.
Martanin ‘yan soshiyal midiya
A halin da ake ciki dai 'yan soshiyal midiya a shafukan sada zumunta sun yi martani kan wannan lamari, inda jama'a da dama suka yi Allah wadai da abin da malamin ya yi.
A martaninsa, Min E Isaac yace:
"Azumin Yesu Almasihu ba azumi ne na gama-gari ba. Ruhu mai tsarki ne ke jagorantar Yesu, kuma ruhu ne ya ba shi ikon yin haka, shi ya sa ya yi nasara."
Simeon Ibe Anusionwu ya ce:
"Irin wannan dogon azumi dole ne Ruhu Mai Tsarki ya umarce ka dashi kuma ya kiyayeka, in ba haka ba za a ji mummunan labari!"
Folorunsho Dan Oliye ya ce:
"Yesu wani ruhu ne wanda ya zo a matsayin mutum, jikinsa daban ne me ya sa fasto zai kwaikwayi abin da Almasihu ya yi."
A wani labarin kunji yadda wani dan kasar waje ya shigo Najeriya da kayan bugarwa, 'yan NDLEA sun kame shi.
Asali: Legit.ng